1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Amirka na yin ziyarar aiki a nahiyar Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 24, 2015

Shugaban kasar Amirka Barack Obama ya isa Nairobi babban birnin kasar Kenya domin fara wata ziyarar aiki ta kwanaki hudu a Afirka.

https://p.dw.com/p/1G4Qu
Hoto: Getty Images/AFP/S. Loeb

Rahotanni sun nunar da cewa daga cikin abubuwan da Obama zai mayar da hankali yayin ziyarar ta sa a kasashen Kenya da Habasha sun hadar da batun yaki da ta'addanci da farfado da tattalin arziki da ma batun kare hakkin dan Adam. Wannan dai shi ne karo na farko da Obaman ke yin ziyara a kasarsa ta asali wato Kenya da kuma Habasha tun bayan da ya zamo shugaban kasar Amirka a shekara ta 2009 ko da yake shine karo na hudu da ya ke ziyara a nahiyar Afirka. Obama dai na zaman shugaban kasar Amirka da ke kan karagar mulki ya kai ziyara a kasar ta Kenya. Tuni dai kakar Obama Sarah Obama da aka fi sani da "Mama Sarah" a kasar ta Kenya ta kama hanyarta ta zuwa Nairobi domin ganawa da jikan nata tare da rakiyar 'yarta Masart Obama. Sara dai na fatan Obama zai je kauyensu na Kogelo domin ya kai ziyara kabarin mahaifinsa. Fadar gwamnati ta White House dai ta ce Obaman ba zai je kauyen nasu ba sai dai Sarah ta ce za ta lallaba shi ya je domin ya ziyarci kabarin mahaifin nasa. A yayin da ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Nairobi, Obama ya samu tarba daga shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta. Kenya dai na fuskantar hare-haren ta'addanci daga kungiyar al-Shabab ta Somaliya a dangane da haka ne ma aka dauki kwararan matakan tsaro a kasar gabanin ziyarar ta Obama.