1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama ya mika godiyarsa ga Putin

Pinado Abdu WabaJuly 16, 2015

Fadar White House ta ce Obaman na mika godiyarsa ne sakamakon rawar da Rashar ta taka wajen tabbatar da nasarar yarjejeniyar Iran.

https://p.dw.com/p/1G01U
Wladimir Putin und Barack Obama am Telefon
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugaba Barack Obama na Amirka ya mika godiyarsa ga takwararsa na Rasha Vladimir Putin sakamakon mahimmiyar rawar da ya ce ya taka wajen tabbatar da nasarar cimma yarjejeniyar makamashin nukiliya da Iran. Fadar shugaba Obaman ce ta sanar da hakan, a baya dai da kyar shugabanin biyu suka amince kan da wannan batu, to amma da wannan cigaban da aka samu, bangarorin na ganin cewa dama ce ta bulla, ta yin aiki tare domin kawo karshen rikicin Yankin Gabas Ta Tsakiya, musamman ma na Siriya.

Rasha dai na daga cikin kasashe biyar na Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, wadanda suke da ikon darewa kujerar naki, to sai dai rikicin Ukraine ya raunana dangantakarta da Amirka ta yadda babu jituwa sosai a tsakaninsu.