1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama ya ziyarci mahaifar kakanninsa, inji jaridun Jamus

Umaru AliyuJuly 31, 2015

Yankin gabashin Afirka ya karbi bakuncin Barack Obama, yayin da ministan tsaron Jamus, Ursula von der Leyen ta yi tattaki zuwa Mali.

https://p.dw.com/p/1G7tf
Äthiopien Addis Abeba Obama Rede Afrikanische Union
Hoto: Getty Images/AFP/S. Loeb

Jaridu da dama, cikinsu har da Tageszeitung da Süddeutsche Zeitung da Neue Zürcher Zeitung duk sun maida hankalinsu ga ziyarar da Barack Obama, shugaban Amirka ya kai kasashen Kenya da Habasha a wannan mako mai karewa. Jaridar Tageszeitung ta duba jawabin Obama ne a gaban wakilan kungiyar hade kan Afirka, wato AU a Addis Ababa. Jaridar tace Obama ya caccaki takwarorinsa na nahiyar Afirka, wadanda ba sa son sauka daga kujerunsu ta mulki ko bayan wucewar wa'adin da doka ta dibar masu. Obama yace babu wani shugaban da ya fi karfin doka a Afirka, inda ma ya kara da cewar democradiya ta kan kasance cikin hadari a duk inda shugaban jama'a ya shiga yin gaban kansa , ko ya shiga take dokokin kasa. Shugaban na Amirka ya kara da cewar bai ga dalilin da kan sanya wasu shugabanni su ci gaba da kafewa kan kujerun mulki ba, musamman idan a tsawon mulkinsu suka tara kudin da ya fi karfin bukatunsu.

Tun kafin ya isa Addis Ababa, sai da shugaba Barack Obama ya ziyarci Kenya, inda jaridar Süddeutsche Zeitung tace shugaban na Amirka ya dawo gida, ya ziyarci kasar da ita ce tushensa. To sai dai wannan ziyara ce ta kasashen biyu masu mulkin kama karya, amma a daya hannun kawayen Amirka. Jaridar tayi tambayar idan ba haka ba, wane dalili Obama din yake dashi na kai ziyara Habasha, kasar da take daga cikin wadanda ke kan gaba a matakan keta hakkin yan Adam da mulkin kama karya a Afirka?

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta duba ziyarar ministar harkokin tsaron Jamus, Ursula von der Leyen a Mali. Jaridar tace von der Leyen ta zabi lokacin da ya dace domin kaiwa kasa ta Mali ziyara. A can din yanzu haka ana ci gaba da aiki da yarjejeniar da aka sanya hannu kanta a watan jiya ta zaman lafiya, tsakani kungiyoyin Abzinawa da gwamnati a birnin Bamako. Kazalika a lokacin ziyararta, Frau von der Leyen ta shaidar da mikawa Jamus aikin jagorancin rundunar hadin gwiwa ta kasashen Turai da Afirka. Wannan runduna ce dake aikin wanzar da zaman lafiya da tauye aiyukan kungiyoyin tarzoma da suka mamaye yankin arewacin Afirka har zuwa kasar ta Mali.

Mali Besuch Bundesverteidigungsministerin Ursula von der Leyen
Minista von der Leyen(hagu) da wakilin MDD a MaliHoto: picture-alliance/dpa/B.v. Jutrczenka

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta duba hare-haren 'yan kungiyar Al Shabaab a Somaliya, inda ta fara sharhinta da taken: ramuwar yan kungiyar Al Shabaab. Tace yanzu dai hukumomi a Somaliya sun dakatar da mafarkin da suke yi cewar zabe a kasar zai yiwu a shekara ta 2016. Hakan kuwa bai samu ba sai da 'yan Al Shabaab suka sanya hukumomin suka farka daga wannan mafarki. Gwamnati da majalisar dokoki sun gane cewar shirin da suka yi na gabatar da kundin tsarin mulki da jama'a za su baiyana ra'ayinsu kansa da kuma gudanar da zabe a shekara ta 2016 ba zai yiwu ba. Bayan fiye da shekaru 20 na yakin haulolin Somaliya, har yanzu lokaci bai yi ba da za'a yi maganar kundin tsarin mulki, ko yiwa wanda aka tsayar a shekara ta 2012 gyara domin gudanar da zabe a shekara mai zuwa.