1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama zai yi balaguron ƙasashen Asiya

November 5, 2010

Kwanaki ƙalilan bayan zaɓen majalisar dokoki da ta dattawan Amirka shugaba Obama yayi haramar ziyarar kasashen Asiya

https://p.dw.com/p/Q08e
Shugaban Amirka Barack ObamaHoto: AP

A gobe asabar ne idan Allah Ya kai mu shugaban Amirka Barack Obama zai sauka kasar Indiya, zango na farko ga ziyarar kwanaki goma da shugaban zai yi ga kasashen Asiya. Muhimmin abin da zai mayar da hankali kansa a ziyarar tasa dai shi ne maganar tsaro da kuma al'amuran ciniki da halin da ake ciki a Afghanistan da kuma tasirin China a yankin kudancin Asiya.

A zamanin baya-bayan nan dai jami'an siyasar ƙasashen yammaci na sha'awar kai ziyara ƙasar Indiya. Babban dalilin haka kuwa shi ne kasancewar tuni China ta sama wani dandalin ayyukan samarwa na duniya a yayinda ita kuma Indiya ta wayi gari a matsayin dandalin ƙaddamar da hidima ga duniya. Tattalin arziƙin Indiya ya samu bunƙasa matuƙai ainun duk da matsalar taɓarɓarewar al'amuran tattalin arziƙin duniya. Kuma kashi 50% na wannan bunƙasar ya samu ne daga ɓangaren ayyukan hidima kamar dai ƙirƙirar da injunan na'ura mai ƙwaƙwalwa. So sai dai kuma Indiya, daidai da ƙasar China, ita ma tana fama da matakan takunkumin ƙasashen yammaci. Amirka na wa Indiya matsin lamba domin daidaita hulɗar ciniki tsakanin ƙasashen biyu. Amirka na buƙatar ganin Indiya na sayen kayayyakinta. Ƙwararrun masana na Indiya dai sun nuna cewar ƙasar na buƙatar kayayyakin fasaha mai zurfi daga Amirka. Amma fa a daidai nan ne take ƙasa tana dabo, saboda Amirka, kawo yanzun, ba ta sha'awar ganin irin waɗannan kayayyaki sun shiga hannun Indiya. An dai samu ci gaban dangantaku tsakanin ƙasashen biyu a baya-bayan nan kuma a saboda haka da yawa daga jami'an siyasar Indiya ke da imanin cewar a halin da ake ciki yanzu ba wani abin da zai hana damar gudanar da irin wannan ciniki, kamar yadda aka ji daga bakin Adi Godrej shugaban jerin kamfanonin Godrej:

"Ta la'akari da ƙaƙƙarfar dangantakar dake akwai a yanzun lokaci yayi da Amirka zata ba mu damar samun fasahohi a dukkan ɓangarorin da suka cancanta. Hakan ka iya zama babban taimako ga tattalin arzƙin Indiya."

Ɗaya buƙatar ƙasar ta Indiya kuma ta shafi manufofin Amirka dangane da Afghanistan. Domin kuwa yaƙin Afghanistan na taimakawa wajen taɓarɓarewar al'amuran tsaro a wannan yanki, lamarin da Indiya ke fama da raɗaɗinsa. Wasu daga cikin mayaƙan Afghanistan na samun horo da goyan baya ne daga Pakistan. Sau tari Pakistan kan yi amfani da waɗannan mayaƙa akan Indiya, kamar dai yadda mahukuntan tsaron Indiyan ke iƙirari. A sakamakon haka tsofon mashawarcin tsaron gwamnatin Indiya Brajesh Mishra ke fatan ganin Amirka tayi wa Pakistan matsin lamba.

"Tuni muka faɗa wa Amirkawa cewar babbar matsalarmu ita ce ta ɗan ta'adda daga Pakistan. Ina kyautata zaton cewar a yanzun Amirka ta kai ganon cewar Pakistan na magana ne da baki biyu-biyu."

Daga cikin batutuwan da Obama zai tattauna a fadar mulki ta New Delhi dai ga alamu har da ma'amalla a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya. Domin kuwa Indiya, daidai da Jamus, tana da mazauni a kwamitin sulhu na majalisar har tsawon shekaru biyu masu zuwa. Wannan ci gaba na daga cikin abubuwan da suka sanya Amirka da Jamus da sauran ƙasashen yammaci su riƙa tuntuɓar ƙasar ta Indiya akai-akai.

Mawallafi: Cem Sey/Ahmad Tijani Lawal

Edita:Abdullahi Tanko Bala