1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Olmert yayi watsi da tattaunawar Sulhu da Hamas

Zainab MohammedDecember 23, 2007
https://p.dw.com/p/CfRy

Primiyan Izraela Ehud Olmert yayi watsi da tattaunawar tsagaita wuta da ƙungiyar Hamas.Daura da haka inji shi dakarun Izraelan zasu cigaba da kai hare hare akan ‚yan kungiyar dake cigaba da harba rokoki zuwa cikin Izraelan daga Zirin Gaza.Olmert yace babu komawa teburin tattaunawa,har sai Hamas ta amince da ka’idoji da bangarorin nan hudu dake shiga tsakani suka gindaya mata.Ɓangarorin hudu da suka hada da Amurka da Rasha da Majalisa Ɗunkin Duniya da Kungiyar Tarayyara Turai,sun bukaci Hamas datayi laakari da Izraela a matsayin ‚yantacciyyar kasa ,tare da watsi da ayyukan tarzoma ,ta hanyar darajawa kwarya-kwaryar yarjejeniyar zaman lafiya na da aka cimmawa.A makon daya gabata dai hare haren Izraelan ya kashe sama da Palastinawa 20.