1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Omar El Beshir ya amince ya gana da wakilyar Georges Bush

August 29, 2006
https://p.dw.com/p/BulE

Shugaba Omar El beshir na Sudan ya amince ya gaba da Jendazi Frazer wakiliyar da shugaba Georges Bush na Amurika ,ya tura a birnin Khartum, domin tanttanawa a game da rikicin yankin Darfur.

Da farko shugaban ƙasar Sudan, ya ƙi amincewa yin ido hudu da wakiliyar ta Amurika, wadda ke ɗauke da saƙo daga Gerges Bush.

Shugaba na Amurika ya bayyana bukatar, Sudan ta amince karɓar rundunar shiga tsakani ta Majalisar Ɗinkin a yankin Darfur.

Bayan da wakiliyar Amurika ta miƙa sakon ga mashawarcin shugaba El Beshir, ya tabatar mata da cewa, Sudan na tsaye kan bakan ta, na adawa da dakarun Majalisar Dinkin Dunia a yankin Darfur.

Za a ganawar ta yau tsakanin Omar El Beshir da Jendayi Frazer bayan shugaban na Sudan ya dawo daga halartar wani taron gangami na nuna goya baya, ga gwamnati a game da matakin da ta ɗauka a rikicin Darfur.

Jikadan Sudan a Majalisar Ɗinkin Dunia,Omar Bashir Mohamed Manis, ya bayyanawa Majalisar matsayin ƙasar sa, a game da wannan batu.