1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

OPEC za ta kara yawan man da take samarwa

Ibrahim SaniNovember 19, 2007
https://p.dw.com/p/CIld

Ƙungiyyar ƙasashe masu arziƙin man fetur ta OPEC, ta yi alƙawarin ci gaba da samar da wadataccen man fetur ɗin a kasuwarsa ta Duniya. Ƙungiyyar ta OPEC ta kuma ɗau gabarar yaƙi da matsalar ɗumamar yanayi, wacce a yanzu ke barazana ga Duniya.Shugabannin ƙasashen na OPEC sun cimma hakanne, a taron ƙolin wuni biyu da su ka gudanarne a birnin Riyad ɗin ƙasar Saudiya. Kafin dai cimma ƙudurorin biyu, an fuskanci banbance banbance a tsakanin mambobin ƙasashen, dangane da ci gaba da wadata man da kuma yadda za a yi hada-hadarsa. Shugaban Iran Mahmud Ahmadinajad ya ce a yanzu haka, OPEC na tunanin sauya kuɗin Dola da ƙungiyyar ke hada-hadar man a kasuwarsa, izuwa wata takardar kuɗin ta daban. Da alama dai hakan nada nasaba ne da yadda ƙudin na Dola ke ci gaba da fuskantar koma bayane.