1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ostiriya zata dakatar da 'yan gudun hijira

Yusuf Bala Nayaya
July 4, 2017

Ministan harkokin tsaron Ostiriya Hans Peter Doskozil ya ce ma'aikatarsa ta shirya aikin jibge dakarun soja da motocin yaki a iyakar Brenner inda baki ke tsallakawa zuwa kasar.

https://p.dw.com/p/2futd
Grenzübergang Österreich - Italien
Hoto: imago/Eibner Europa

Ministan harkokin wajen  Ostiriya Sebastian Kurz ya bayyana cewa kasar a shirye take ta kare iyakokinta da Italiya a daidai lokacin da kasar ta lura cewa Italiya na kara samun 'yan gudun hijira da ke tudada zuwa kasar, abin da zai iya sawa idan sun yi yawa su kutsa cikin kasarta. Kurz ya bayyana haka ne ga kamfanin dillancin labarai na Ostiriya a wannan rana ta Talata yayin da aka fara shirye-shirye na daukar matakan kulle iyakar.

Ministan harkokin tsaron Ostiriya Hans Peter Doskozil ya ce ma'aikatarsa ta shirya aikin jibge dakarun soja da motocin yaki a iyakar Brenner inda ake samun masu tsallaka iyaka tsakanin kasashen biyu, ya kuma ce nan da sa'oi 72 ne za a iya fara aikin. Jami'an suka bayyana cewa duk da cewa babu fargabar barkowar 'yan gudun hijirar yanzu amma dai Italiya da Kungiyar Tarayyar Turai suna sane da cewa a shirye muke mu kare iyakarmu ta Brenner.