1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

140509 Nazareth Papst

May 14, 2009

A garin Nazareth Paparoma Benedikt na 16 ya jagoranci wani bikin addu´o´i mafi girma a ziyarar kwanaki takwas da yake kaiwa yankin Gabas Ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/HqQA
Paparoma Benedikt na 16 yana jagarontar bikin addu´o´i a NazarethHoto: AP

A huɗubarsa, Paparoma ya jaddada muhimmancin rawar da iyali ke takawa a matsayin ginshiƙin wannan al´uma ta yau. Shugaban na mabiya ɗarikar Katholika ya kuma yi kira ga mabiya addinan Kirista da Musulunci da su samar da kyakkyawar zamantakewa tsakaninsu.

Paparoma Benedikt na 16 ya samu kyakkawar tarba a garin na Nazareth, inda dubban mabiya addinin Kirista suka hallara don sauraron huɗubarsa suna ta shewa suna cewa kamar Paparoma John Paul kai Benedikt muna ƙyaunarka. Allah Ya ja zamaninka.

A cikin huɗubarsa Benedikt ya yaba da garin na Nazareth a matsayin wani wuri na iyalai tsarkakku. Ya bayyana rayuwar Maryam da Yusif da kuma Annabi Issah (A.S.W.) a matsayin abin koyi ga dukkan jama´a. Kamar hurucin da Paparoma Paul na shida ya yi a wannan wuri shekaru 45 da suka gabata shi ma Benedikt ya ce yana da muhimmanci a riƙa kai ziyarar ibada a Nazareth don ganin yadda iyalai tsarkakku suka rayu. Paparoma ya jaddada muhimmiyar rawar da mace ke takawa a zamantakewar iyali da kuma al´uma.

"Nazareth na yi mana tuni da muhimmanci da daraja da kuma rawar da mace ke takawa tare da girmama irin basirar da Allah Ya ba ta. A matsayinta na uwa a cikin iyali ko ma´aikaciya a wurin aiki ko a cikin al´uma ko wajen yaƙi da talauci, ba za mu iya kimanta muhimmiyar rawar da mace ke takawa ba."

Iyali dai shi ne ginshiƙin samun kyakkyawar al´uma inji Paparoma, wanda kuma ya yaba da hukuma wadda ke tallafawa iyali musamman wajen ba da tarbiya ta gari.

Benedikt ya girke tubalin gina wata cibiya ta ƙasa da ƙasa don tallafawa iyali a Nazareth. Da wannan tubalin Paparoma ya kawo ƙarshen bikin shekarar Iyali a ƙasa mai tsarki. Manufa dai ita ce ƙarfafa wanzuwar Kirista a ƙasa mai tsarki da dakatar da ƙaurar da kiristocin ke yi daga Isra´ila da kuma yankunan Falasɗinawa.

Shugaban na mabiya ɗarikar Katholika ya kuma tofa albarkacin bakinsa dangane da tashe tashen hankula da a kan samu lokaci zuwa lokaci tsakanin Kirista da Musulmai a a Nazareth.

"Ina kira ga mabiya waɗannan addinai biyu da su ɗinke ɓarakar dake tsakaninsu. Dukkanmu mun yi imani ga Allah guda ɗaya Ubangijin talikai. Dole a yi aiki tuƙuru don samar da zaman lafiya da kyakkyawar zamantakewa tsakani."

A ƙarshen jawabinsa Paparoma ya yi addu´o´i a babbar majami´ar garin na Nazareth sannan ya gana da shugabannin addini na lardin Galiläa dake arewacin Isra´ila, sannan a ƙarshe yake gana da Firaministan Isra´ila Benjamin Netanyahu.

Mawallafa: Sebastian Engelbrecht/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu