1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma ya kammala ziyararsa zuwa Turkiya

Hauwa Abubakar AjejeDecember 1, 2006

.:A yau Paparoma Benedict na 16,yake kammala ziyarasa zuwa kasar Turkiya,a kokarinsa na neman sasantawa tsakanin alummar musulmi a daya hannun kuma da tsakanin darikar Orthodox day an Katolika a koina cikin duniya.

https://p.dw.com/p/BtxF
Paparoma tare da Cagrici
Paparoma tare da CagriciHoto: AP

A yau Paparoma Benedict na 16,yake kammala ziyarasa zuwa kasar Turkiya,a kokarinsa na neman sasantawa tsakanin alummar musulmi a daya hannun kuma da tsakanin darikar Orthodox day an Katolika a koina cikin duniya.

Paparoman ya kaddamar da wannan ziyara ce kwanaki hudu da suka shige,wadda ake ganin wani yunkuri ne na neman sulhu tsakanin fadar Vatican da alummar musulmi,game da kalaman da yayi da suka tunzura musulmi baki daya.

A ziyarar tasa dai Paparoma Benedict na 16, dan shekaru 79 da haihuwa yayi ta yabawa Turkawa dama aluammar musulmi wanda yace ya kamata su zauna lafiya tsakaninsu da sauran addinai,inda yace addainan guda biyu suna da alaka da juna.

A jawabansa paparoman yayi kokarin wajen kare furta kalamai masu rikitarwa da zaayiwa fassara su da wata manufa ta daban.

A rana ta karshe ta ziyara Paparoman ya gudanar da taron adduoi da yan darikar katolika dake Turkiyan.

Inda ya sake nanatawa alummomin musulmi cewa cocin katolika bata da aniyar tilasata wani abu akan kowane mutum.

Paparoman yayi iyaka kokarinsa na ganin ya baiwa musulmi tabbacin cewa,manufarsa itace ta neman hadin kai a maimakon ja da juna,sai dai ya baiyana a fili cewa ya kamata kasashen musulmi su inganta harkokin yancin yan adam kan kananan alummomin kiristoci dake cikinsu.

A jiya rana ta uku ta ziyarar tasa Paparoman ya ziyarci masallcin daular usmaniya da aka gina a karni na 17,inda ya gudanar da adduoi tare da babban shehun malami na Ankara Mustafa Cagrici.

Karo na biyu ke nan da wani Paparoma ya taba kai ziyara cikin masalaci,a ziyara ta farko Paparoma John Paul na 2 ya kai ziyara wani masalci a birnin Damascus na kasar Syria.

Paparoma Benedict na 16,ya kuma yi kokarin sasantawa da yan cocin Orthodox,inda ya tattauna da shugaban cocin na Turkiya Bartholomew na 1 a kokarinsa na cike gibi dake tsakanin cocin biyu.

Inda yace ya kamata alummar turai su farfado da addinin kirista a nahiyar.

A gaba daya dai akwai alamun cewa wannan ziyara ta Paparoma ta samu nasara kwarai da gasket kasancewar manyan jaridun Turkiya a yau sun yaba da yadda ya tsaya a masallaci yayi aduoi tare da alummar musulmi.