1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma ya samu kyakyawan tarbe a Amirka

Gazali Abdou tasawaSeptember 23, 2015

Mutane kimanin dubu 15 ne Shugaban Obama ya gayyata a fadar tasa domin tarbon babban bakon nasa a wannan ziyara mai cike da tarihi da ta kasance ta farko da Paparoman ya kai a fadar shugaban kasar ta Amirka.

https://p.dw.com/p/1GbqI
USA Washington Besuch Papst Franziskus mit Obama
Hoto: Reuters/K. Lamarque

Paparoma Francois ko Francis jagoran Kristoci mabiya darikar Katolika ya isa kasar Amirka a wannan Laraba inda ya samu kyakyawan tarbe daga Shugaban kasar ta Amirka Barack Obama a fadarsa. Yau watanni da dama kenan dai da birnin Washington ya dau harami domin tarbar babban bakon a wannan ziyarar mai cike da tarihi da ta kasance ta farko da ya kai a fadar shugaban kasar ta Amirka.

Shugaba Barack Obama ya bayyana matukar farin cikinsa da wannan ziyara ta Paparoma Francois, mutuman da ya ke matukar bege musamman ganin irin rawar da ya ke takawa wajan kyautatuwar hulda tsakanin kasar ta Amirka da ta Kuyba, wacce ta ke daya daga cikin muhimman manufofin diplomasiyyar ketare ta Shugaba Obama a daidai lokacin da ya rage kasa da kwanaki 500 wa'adin milkinsa ya kawo karshe.

Mutane kimanin dubu 15 ne Shugaban Obama ya gayyata a fadar tasa domin tarbon babban bakon nasa dama karramasa.