1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paris: Ana cigaba da farautar 'yan fashi

Ahmed Salisu
January 11, 2018

Jami'an tsaro a birnin Paris na Faransa sun ce suna cigaba da gudanar da bincike tare da farautar wasu mutane da ake zargi da yin fashi a wasu shaguna na Otel din Ritz inda aka sace sarkoki da wasu kayan kawa masu tsada.

https://p.dw.com/p/2qfMf
Raubüberfall Ritz Hotel in Paris
Hoto: picture-alliance/dpa/Maxppp/O. Corsan

Ya zuwa maraicen jiya Laraba, 'yan sanda sun ce sun kama mutum 3 da ake zargi da hannu a fashin kuma suna cigaba da neman karin wasu mutane da ake tunanin suna da hannu a fashin da aka yi a tsakiyar birnin na Paris.

Gidan talabijin din BFM da ke Faransa ya ce darajar kayan da aka sace ta kai sama da dalar Amirka miliyan 5 kuma ya zuwa yanzu ba a kai ga tantace ko 'yan sanda sun samu sukunin samo wasu daga cikin kayan da aka sace ba.

Birnin na Paris dai ya yi kaurin suna wajen aikata irin wadannan manyan laifuka da suka hada da sata da kuma fashi da makami.