1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pierre Schorri ya yi jawabin ban kwana da Cote d` Ivoire

January 31, 2007
https://p.dw.com/p/BuSq

Shugaban tawagar Majalisar Ɗinkin Dunia a Cote d`Ivoire, Pierre Schorri, ya gana yammacin jiya da manema labarai, a birnin Abidjan.

Jami´in, ya yi kira da babbar murya, ga ƙasashe da ƙungiyoyi masu faɗa a ji, na dunia, su ƙara himmantuwa wajen kawo ƙarshen rikicin wannan ƙasa da ya ƙi ci ya ƙi cenyewa.

Pierre da zai barin kasar nan da sati 2 masu zuwa, ya bayyana takaicin kasawar da yayi wajen warware wanan rikici, a tsawan shekaru 2 da ya rike mukamknsa a kasar.

Sannan ya ƙara jan hankula da cewar, idan rikicin Cote d´Ivoire ya ci gaba, ƙasar zata faɗa cikin masifa, a yan kwanaki masu zuwa, ta la´akari da taɓabarewar tattalin arziki da ke bazuwa kamar wutar daji a ko inna cikin ƙasar.