1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu shugar da kara sun wanke Platini

Zainab Mohammed Abubakar
May 26, 2018

Tsohon shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta Turai Michel Platini, ya yi kira ga hukuma wasan kwallon kafa ta duniya FIFA da ta dage dakatar da shi da aka yi a kan badakalar kudi euro miliyan 1.8 da ya karba a 2011.

https://p.dw.com/p/2yNe0
Michel Platini
Hoto: Getty Images/P. Schmidli

Kiran ya biyo bayan sanarwar data fito daga wajen masu shigar da kara na kasar Switzerland a wannan Asabar, da ke nuni da cewar, babu wata shaida data tabbatar da zargin da ake wa Platini.

Lauyan da ke kareshi Vincent Solari, ya ce a yanzu haka an wanke tsohon shugaban hukumar wasan kwallon kafar Turan, don haka babu wata shari'a a kansa. Sai dai ofishin masu shugar da karar da ke Switzerland, ya nunar da cewar, za'a cigaba da gudanar da bincike a kan Platini.

A shekara ta 2015 nedai hukumar FIFA ta dakatar da Michel Platini daga shiga duk harkokin  wasan kwallon kafa har na tsawon shekaru takwas, ka na daga bisani ta rage zuwa hudu, dangane da bakadalar dalar Amurka miliyan biyu da ya karba daga hukumar FIFa a 2011.