1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Praministan Irak ya yi watsi da matakin Majalisar dattawan Amurika na raba Irak gida 3

September 29, 2007
https://p.dw.com/p/Bu9u

Praministan ƙasar Irak Nuri Al Maliki ya yi watsi da dokar da Majalisar datawan Amurika ta rattaba wa hannu, wace ta tanadi kasa Irak a yakunan 3 masu cikkaken yanci.

A cewar Al Maliki, al´umomin ƙasar Irak kaɗai ke da hurumin ɗaukar irin wannan mataki ba Amurika ba.

Raba Irak gida 3, zai hadasa wata babbar fitina, a yankin baki ɗaya, inji Praministan.

Majalisar dattawan Amurika, ta tsara girka ƙasashe 3 tsakanin ƙurdawa, yan sunni da yan schi´a.

A tunanin wannan majalisa, karkasa Irak gida 3, shine zai kawo ƙarshen tashin hankali a wannan ƙasa.

Nuri Al Maliki ya yi kira ga yan majalisar dokokin Irak, su shirya taro na mussamman, domin hido sanarwar yin Allah wadai da wannan tsarin na Majalisar Dattawan Amurika.