1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Praministan Korea ta Kudu yayi murabus

March 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bv57
Steinmeier
SteinmeierHoto: AP

Shugaban ƙasar Corea ta kudu, Roh Moo-Hyun, ya amince da murabus ɗin, da Praministan sa, ya gabatar masa.

Lee-Hae –Chan, da ke matsayin Pramisita, tun watan juni na shekara ta 2004, na fuskantar zargin cin hanci da karɓar rashawa.

Jam´iyun adawa, a yan kawanakin nan,sun matsa lamba, da girka komitin bincike, domin gano gaskiya, a kan zargin da ke wa Praministan.

Masu kula da harakoki siyasa a ƙasar, na hasashen cewa, wannan al´ammari, zai hadasa koma baya, ga jami´yar Uri, mai rike da ragamar mulki, a yayin da, ya rage yan kawanaki ƙalilan, a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi, a Corea ta kudu.