1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Premier Ehud Olmert ya bada shaida adangane da yaki da Hizbollahi

February 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuSe

Prime minista Ehud Olmert na kasar Izraela ya fara bada bayanan shaida a gaban wata hukuma ta musamman da gwamnatin kasar ta nada ,domin binciken yakin da dakarun Izraelan suka kaddamar akan yan Hizbollahi din kasar Lebanon a shekarar data gabata.Gwamnatin Izraela da dakarunm sojin kasar dai na fuskantar mummunar suka dangane da yadda wannan fada na wata guda ya gudana.Prime minista Olmert dai na mai zama na karshen shaidu kimanin 70 dasu bayyana a gaban wannan hukuma,wadda zata gabatar da kwarya kwaryar rahotanta a tsakiyan watan Maris mai kamawa.