1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Prodi ya lashe zaben Italia

Zainab A MohammadApril 19, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6r

ITALY

A yau ne kotun kolin Italia ,ya tabbatar da Romano Prodi na jammiyar matsakaitan gurguzu ,da kasancewa wanda ya samu nasara a zaben daya doke Prime minista Silvio Berlusconi,a zaben kasa baki daya daya gudana a makon daya gabata.Sanarwar tabbacin sakamakon zaben da kotun kolin tayi a birnin Rome,yazo ne bayan an kammala kidayar sauran kuriu 5,000,wadanda baa kidayasu ba alokacin kidayan ,kuriu da aka kada alokacin zaben.A na kyautata zaton dai wannan sanarwa zai kawo karshen takaddamar siyasa dake tsakanin bangarorin biyu,tare da bawa Mr Prodi damar kafa sabuwar gwamnati a wata mai zuwa.Premier Berlusconi dai yaki amincewa da kayen daya sha bisa ga sakamakon zaben,inda yake zargin cewa an tabka magudi.

A taron manema labaru daya gudanar bayan sanarwar,Romano Prodi yayi alkawarin aiki cikin gaskiya da adalci,bisa ga goyon baya da alummar kasarsa suka basi.Mr Prodi mai shekaru 66 da haihuwa,yace a yanzu dai Italia zata kama madafa a dangane da kafa sabuwar gwamnati.