1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Puigdemont: Ba zan nemi shugabanci ba

Yusuf Bala Nayaya
March 2, 2018

Korarren shugaban yankin Kataloniya Carles Puigdemont ya ajiye shirinsa na neman a sake zabarsa a matsayin shugaban yankin, yayin da ya nuna wani dan siyasar yankin na Kataloniya da a yanzu ke gidan wakafi ya gaje shi.

https://p.dw.com/p/2tYxC
Videostill aus einer Videorede von Carles Puigdemont
Hoto: Reuters/Handout

Puigdemont ya ce ya yanke shawarar koma wa gefe na dan wani lokaci don ya ba da dama ga wani ya jagoranci yankin a daidai lokacin da yake ci gaba da zaman neman mafaka a Beljiyam. Ya ce wannan mataki shi ne kawai zai bude kofa a kai ga kafa sabuwar gwamnati a yankin na Kataloniya.

Shi dai Puigdemont ya nuna Jordi Sanchez ya karbi jagorancin tafiyar, kasancewar Sanchez fitaccen dan siyasa da ke kan gaba a fafutkar ganin yankin na Kataloniya ya samu 'yancin gashin kai wanda kuma a halin yanzu ke a gidan kaso a birnin Madrid bisa zargin shirya tawaye ga mahukuntan Spain.

Yanzu dai yankin na Kataloniya ana mulkarsa ne daga Madrid tun bayan da Firaminista Mariano Rajoy ya karbi iko biyo bayan da yankin ya ayyana cin gashin kai a watan Oktoba.