1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'ayin Checheniyawa A Jamus A Game Da Tsautsayin Beslan

September 13, 2004

Checheniyawan dake neman mafaka a nan jamus sun bayyana kaduwarsu a game da ta'asar garkuwa da 'yan makaranta da aka fuskanta a Beslan kwanaki goma da suka wuce

https://p.dw.com/p/BvgY

Yawa-yawancin ‚yan usulin Checheniya dake gudun hijira a nan Jamus, ko da yake sun kadu da tsautsayin da ya rutsa da kananan yara ‚yan makaranta da aka yi garkuwa dasu a Beslan, amma a daya bangaren sun tababa a game da gaskiyar bayanan da mahukuntan Rasha suka bayar a game da wannan mataki na ta’addanci. A lokacin da yake bayani game da haka wani dan usulin Chechniya mai suna Issa dake da shekaru 40 da haifuwa yake kuma neman mafakar siyasa a nan Jamus tun misalin shekaru uku da suka wuce ya ce dukkan abokansa sun kadu da abin da ya wakana a Oseshiya dake makobtaka da kasarsu, wanda a ganinsu mummunan dannyen aiki ne da ba za a iya musulta shi ba. Ya ce ko da yake akwai mummunar kiyayya ga sojojin Rasha a zukatan Chechniyawan, amma wannan mataki na rashin imani da aka dauka tilas ne a yi Allah Waddai da shi. Bugu da kari kuma tun da ake ba a taba samun rikici ko wata matsala a dangantakar Oseshiya da Checheniya a cikin tarihin sassan biyu dake makobtaka da juna ba. A saboda haka Chechniyawan ke tababa a game da bayanai da mahukuntan Rasha suka bayar dangane da masu alhakin wannan danyyen aiki na garkuwa da ‚yan makaranta. A hukumance dai an yi ikirarin cewar Checheniyawa shida da Ingushiyawa hudu sune suka kai farmakin a Beslan suna masu halaka mata da yara kanana. In har ana fatan tsage gaskiyar lamari to kuwa wajibi ne a kafa wata hukumar bincike mai zaman kanta da zata yi bi diddigin ainifin abin da ya faru, amma mahukuntan Rasha sun ki amincewa da haka. Yau kimanin shekaru goma ke nan al’umar Chechniya na fama da wahala sakamakon yakin da Rasha ta gabatar akan kasarsu, wannan shi ne dalilin da ya sanya akasarin Chechniyawa ke ba da cikakken goyan baya ga ‚yan tawayen kasar. Akwai kiyayya mai tsananin gaske a zukatansu akan sojojin Rasha. To sai dai kuma wannan kiyayyar bata kai matsayin da Checheniyawan zasu ba da goyan baya ga ta’asar zub da jinin da ta wanzu a Beslan ba. Shi kansa shugaban ‚yan tawayen kuma tsofon shugaban Checheniya Aslan Mas’chadov ya musunta zargin cewar kungiyarsa na da hannu a wannan ta’asa ta garkuwa da ‚yan makaranta, ko da yake daya madugun ‚yan tawayen mai tsananin kishin addini Schmail Bassayev har yau bai ce uffan ba. Ainifin abin dake akwai, kamar yadda wani dan usulin Checheniya dake neman mafaka a Berlin ya nunar, da zarar an fuskanci tsautsayi a Rasha sai mahukunta su rika bakin kokarinsu wajen dora laifin akan Checheniyawa saboda kawar da hankalin jama’a daga ainifin matsalolinta na cikin gida. Tun da jimawa ake rade-radi a game da yiwuwar cewa hukumar leken asirin Rasha na da hannu akan wasu hare-hare na ta’addancin da akan dora laifinsu akan ‚yan Checheniya. Ita dai ta’asar ta garkuwa da ‚yan makaranta ta kada zukatan Checheniyawan dake nan Jamus, wadanda ke tababa a game da bayanai da mahukuntan Rasha suka bayar kuma a saboda haka suke fargaba a game da cewar rikicin kasarsu zai dada yin tsamari domin kuwa dukkansu sun baro dangi da abokan arziki a can Checheniya.