1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

RA'AYIN `YAN GUDUN HIJIRAN KASAR TOGO GAME DA MUTUWAR EYADEMA

Yahaya AhmedFebruary 10, 2005

Ban da dai Faransa, a Jamus ne mafi yawan `yan gudun hijiran Togo suka sami mafakar siyasa. Hakan kuwa na da jibinta ne da tarihi da kuma dalilan siyasa da suka hada kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/BvdF
Tutar kasar Togo

Da farko dai `yan gudun hijiran kasar Togo da ke zaune a birnin Hamburg a nan Jamus, sun nuna shakkunsu ga labarin mutuwar tsohon shugaban kasar Gnassingbe Eyadema. Dalilin haka kuwa shi ne, a cikin `yan shekarun da suka wuce ma, an yi ta yada rade-radin mutuwarsa. Amma da labarin ya tabbata a wannan karon, sai makauratan na Togo suka yi ta murna da hakan. Wasu `yan kasar da wakilinmu Thomas Mönch ya yi fira da su a birnin Hamburg, sun bayyana ra’ayoyinsu ne kamar haka:-

"Ni ma dan Adam ne, shi ya sa na yi wa ransa fatan alheri na kuma yi fatar samun `yancin walwalar jama’a a kasararmu."

"Ni dai zato na yi cewa hakan yana da kyau, yanzu za mu sami kasa mai kare k`yancin al’ummanta."

"Ni da na ji labarin, sai na yi ajiyar zuciya na ce: barakallah, yanzu dai ya tafi, al’ummanmu za su sami `yancin sakewa."

Akwai dai shahararrun masu fafutukar kare hakkin dam Adam da dama daga kasar Togon, wadanda ke zaman gudun hijira a nan Jamus, saboda fatattakarsu da gwamnatin shugaba Eyadema ke yi. daya daga cikinsu shi ne Bozoura Gandi, wanda tun shekaru biyu da suka wuce ne ya yi kaura zuwa Hamburg inda kuma aka ba shi mafaka. A cikin shekarar 1997, sai da Eyadema ya sa aka daure shi a kukrkuku har tsawon shekara daya da rabi, ba tare da an yi masa shari’a ba. Ya dai bayyana ra’ayinsa game da Eyademan ne da cewa:-

"Wannan mutum in Eyadema, wato ya kasance kamar wata anoba ne ga kasar Togo. Shekaru 23 a jere muka shafe muna ta fama karkashin mulkin danniya. A cikin shekarar 1990 ne dai al’umman kasar suka ta da kayan baya, saboda abin ya ishe su. Daga nan ne muka fara gwagwarmaya."

Gwagwarmayar da `yan kasar suka yi dai, ta hannunka mai sanda ce. Amma duk da haka, an cim ma nasara, inda ba da sonsa ba, Eyadema ya amince da kafa jam’iyyun siyasa daban-daban. Sai dai, ya yi duk iyakacin kokarinsa wajen ganin cewa ya zarce da mulki.

Wani dan gudun hijiran, Inoussa Ousmane Yekini, wanda wakilinmu ya yi fira da shi, ya bayyana cewa, nada dan Eyademan a mukamin shugaban kasa da sojin kasar suka yi, wato wani yunkuri ne na tabbatad da iyalin Eyademan dindindin a kan ragamar mulkin kasar. Shi dai Ousmane Yekini, shi ke wakilcin jam’iyyar adawar kasar Togon a nan Jamus, jam‘iyyar da Gilchrst Olympio ya kafa. Tun shekaru 12 da suka wuce ne Yekinin ke zaune a birnin Hamburg, tamkar dan gudun hijira. Game da mulkin Eyademan dai, ya bayyana cewa ba ya iya tuna wani abu mai faranta rai:-

"Da nake karami na halarci makaranta a barikin soji. Zan iya tuna wani lokaci da malamin ya shigo aji da libarba, inda ya yi ta ba mu tsoro da ita. Ni kam ba na son `ya`yana su ga irin wadannan ababan a rayuwarsu."

Duk maneman mafakan Togon dai na kira ga aal’umman kasar da su hada kai wajen daddagewa sabbin shugabannin kasar, su nuna kin amincewarsu da nada dan shugaban Eyademan a mukamin shugaban kasa da aka yi. Suna dai ganin wannan matakin tamkar wani shiri ne na juyin mulki a fakaice.

Mafi yawan `yan kasar Togon da aka yi fira da su, sun nanata cewa, kamata ya yi kasashen ketare ma su tsoma baki a cikin wannan lamarin don angaza wa mahukuntan kasar su bi ka’idojin da kundin tsarin mulkin kasar ya shimfida. Sun dai nuna gamsuwarsu da matsayin da kasashen Afirka da kuma wasu kasashen Turai suka dauka a kan wannan batun.

Suna kuma fatar cewa, Jamus, wadda ta yi wa kasar mulkin mallaka, za ta yi duk iyakacin kokarinta wajen ganin cewa, an tabbatad da mulkin dimukradiyya a kasarsu ta asali.