1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'ayin `yan siyasan Jamus game da jawabin shugaba Chirac

January 20, 2006

Jami'an siyasa na manyan jam'iyyun da ake wakilcinsu a majalisar dokokin Jamus, sun mai da martani ga jawabin da shugaba Chirac na kasar Faransa ya yi, na yin amfani da makaman nukilyan kasarsa wajen afka wa kasashen da ya kira na `yan ta'adda, idan bukata ta kama. Ra'ayoyi dai sun bambanta a kan wannan batun.

https://p.dw.com/p/Bu2F
Shugaba Chirac na Faransa.
Shugaba Chirac na Faransa.Hoto: AP

Jawabin da shugaban Faransa Jacques Chirac ya yi, game da yin amfani da makaman nukiliyan kasarsa wajen afka wa kasashen da ya kira na `yan ta’adda, ya janyo wata muhawara a birnin Berlin, wato fagen siyasar Jamus, inda aka sami ra’ayoyi da dama, wadanda suka bambanta. Duk da cewa dai gwamnatin tarayya, ba ta fito fili ta bayyana matsayinta a kan wannan batun bisa manufa ba, wakilan jam’iyyun siyasa a majalisar dokoki ta Bundestag, sun yi ta bayyana nasu ra’ayoyin. Kakakin jam’iyyun `yan mazan jiya na CDU da CSU a majalisar, mai kula da batutuwan da suka shafi harkokin waje, Eckard von Klaeden, ya bayyana ra’ayinsa game da jawabin shugaban Faransan ne kamar haka:-

„Jawabin shugaban na Faransa dai, ya zo ne a lokacin da bai dace ba. Saboda a halin yanzu, ita Faransan da Birtaniya da kuma Jamus na ta kokari ne tare da hadin gwiwar Amirka, wajen janyo Rasha da Sin a bangarensu, don su iya shawo kan Iran ta dakatad da shirye-shiryenta na mallakar makaman nukiliya.“

Wani dan siyasan jam’iyyar CDU, Ruprecht Polenz, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin harkokin waje na majalisar dokokin ta Jamus, yana ganin jawabin shugaba Chirac ne tamkar wani yunkuri da Faransan ke yi, wajen sauya manufofin nukilyanta da ta tsara tun lokacin yakin cacar baka, don su kunshi matakan huskantar sabuwar barazanar da ta’addanci da kuma yaduwar makaman kare dangi ke kalubalantar duniya da su. Shugaba Chirac dai, ya nanata cewa, nan gaba ma, makaman nukilyan za su kasance makamai ne na hakon juna, amma ba na yaki ba.

Su ko `yan jam’iyyar SPD, sun nisantad da kansu ne daga goyon bayan jawabin shugaban Faransan. Kamar yadda kakakin jam’iyyar a kan batutuwan da suka shafi harkokin waje da na tsaro, Walter Kolbow, ya bayyanar, daukan matakan riga kafi don hana hare-haren `yan ta’adda, wani abu ne mai ma’ana kuma mai muhimmanci, amma bai dace a ce da makaman nukilya, za a wanzad da su ba:-

„Kwance damara, da kaucewa daga yin amfani da makaman nukilya na cikin kudurorin manufofin siyasar da gwamnatinm hadin gwiwa ta manyan jam’iyyu ta amince da su. Sabili da haka, mu `yan jam’iyyar Social Democrats, ko kadan ba mun amince da jawabin da shigaba Chirac ya yi na yin amfani da makaman nukiliyan, idan bukata ta kama ba.“

Su ko `yan jam’iyyun adawa a majalisar, ba su yi rufa-rufa ba, ba wajen yi wa jawabin shugaban na Faransa kakkausar suka. Shugaban jam’iyyar FDP, Guido Westerwelle, ya bukaci shugaban gwamnatin tarayya Angela Merkel ne, da ta buga wa shugaba Chirac waya kai tsaye don ta ba shi shawarar yin taka tsantsan a kan batun yin amfani da makaman nukiliyan. Ita ko shugaban jam’iyyar Greens a majalisar, Claudia Roth, cewa ta yi, jawabin Chirac zai janyo dusashewar kwarjinin da kungiyar Hadin Kan Turai ke da shi a idanun duniya ne, dangane da manufofinta na cim ma kwance damarar makaman nukiliya:-

„Shugaban na bayyana abin da shugabannin Iran ke son ji ne. Yanzu dai za su iya hujjanta fafutukarsu ta sarrafa nasu makaman nukilyan da wannan jawabin. Ina dai kyautata zaton cewa, gwamnatin tarayya za ta bayyana matsayinta game da wannan batun a zahiri, saboda batun wato kasada ce ta nukiliya.“

Kazalika jam’iyyun neman sauyi a majalisar, su ma sun bukaci gwamnatin tarayya da ta nisantad da kanta daga wannan matsayin da Faransa ta dauka, inda suka ce wajibi ne a dau matakan shawo kan Faransan da ta kauce daga wannan manufar.