1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra´ayoyi a game da belin likitocin Bulgaria a Lybia

Yahouza S. MadobiJuly 24, 2007

Ƙasashe na ci gaba da huruci a game da sallamar likitocin nan yan ƙasar Bulgaria da da kotun Lybia ta tsare tsawan shekaru fiye da 8

https://p.dw.com/p/Btux
Hoto: picture alliance/dpa

Ƙasashe da ƙungiyoyi daban-daban na dunia, na ci gaba da huruci, a game da belin nas-nas ɗin nan guda 5, yan ƙasar Bulgaria, da Dokta ɗaya na Palestinu, wanda wata kotun Lybia ta yankewa hukuncin kissa, a dalili da tuhumar su da a hukumomin ƙasar su ka yi, da ɗuga ƙwayoyin cutar Aids ga ɗaruruwan yara.

Yahouza Sadissou Madobi ya tattaro mana wasu daga wannan huruce-huruce.

Ƙungiyar gamayya turai ,na sahun gaba daga sahun ƙasashen da su ka bayyana matuƙar gamsuwa da wannan beli.

Jim kaɗan bayan samun labarin, sakataran zartaswa na EU, Jose Manuel Barrosso, ya gabatar da jawabi, inda ya bayyana matsaya ƙungiyar tarayya turai a game da wannan rana, da ya dangata da ranar farin ciki.

Shugaban ƙasar France,Nikolas Sarkozy wanda matar sa Cecilia , ta yi rawar gani a wannan yaƙi, ya ce tun daga gobe zai je ƙasar Lybia domin kai gaisuwa ga shugaba Khaddafi, a game da amincewar da yayi, ta yiwa wannan likitoci afuwa, da kuma sallamar su zuwa ƙasashen su na asuli.

A taron manema labarai da ya kira a kann wannan batu,a fadar Elysee ta birnin Paris,Sarkozy ya ce ƙasar Qatar itama ta cencenci yabo, a cikin wannan al´amari, domin ta alkawarta biyan baki dayan kudin diyyar da a ka zuba domin samun afuwa ga likitocin.

A fagen siyasar France , kussan jam´iyun ƙasar baki ɗaya, sun bayana sanarwoyi, inda su ka yaba wannan ƙoƙari na shugaban Sarkozy.

A yayin da ya ke na sa hurucu, Gernot Erler shugaban hukumar hulɗoɗi da ƙasashen ƙetare ta ƙasar Jamus shima ya nuna gamsuwa.

Shima kakakin opishin ministatan harakokin wajen Amurika ,ya danganta belin likitocin a matsayin wani mataki na samun haɗin kan kasar Lybia.

Sean Mac Cornack ya ce babu shjaka wannan mataki zai sa ƙasashen dunia dubi Lybia da idon rahama ta fannin hulɗoɗin diplomatia.