1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra´ayoyi a game da rasuwar Mr Milosevic

Ibrahim SaniMarch 13, 2006

Da alama rasuwar Mr Milosevic na neman haifar da rudani na siyasa a sabiya

https://p.dw.com/p/Bu1A
Hoto: AP

Rahotanni sun nunar da cewa jim kadan da bayar da sanarwar mutuwar Slobodon Milosevic, daruruwan magoya bayan sa ne suka yi jerin gwano a kofar babban ofishin Jam´iyyar sa dake tsakiyar Belgrade don nuna alhinin su da kuma ta´aziyyar su.

Mutanen wanda da yawa yawan su mutane ne da suka manyan ta, sun kuma saka hannu akan littafin ta´aziyya da aka ajiye a kusa da wani katafaren hotun mamacin.

Da yawa daga cikin mutanen sun bayyana Slobodon Milosevic a matsayin grwaron namiji da yayi wa kasar sa aiki tukuru a lokacin yana raye.

Bugu da kari, a wani taron gaggawa da jam´iyyar sa ta SPS ta gudanar don mika ta´aziyyar su ga iyalan mamacin, daya daga cikin jami´an jamiyyar mai suna,Ivica Dacic yace Milosevic ba mutuwar Allah da annabi yayi ba,domin kuwa kashe shi akayi a cikin gidan yarin da ake tsare dashi.

Za´a iya gane hakan ne a cewar Mr Dacic ta kin yarjewa tsohon shugaban zuwa birnin Mosko neman magani daga bangaren kotun da take tuhumar Mr Milosevic.

Jamiyyar ta SPS, ta tabbatar da cewa zata ci gaba da tuna Mr Slobodon Milosevic a matsayin gwarzo da yayi aiki tukuru wajen kasancewar kasar tsintsiya daya madaurikin ki daya, a hannu daya kuma da kasancewar sa a matsayin mai fafutikar kare hakkin bil adama.

Suma dai jaridun kasar Serbiya , ba a barsu a baya ba, domin kuwa da yawa daga cikin su sun zargi kotun kasa da kasar ce dake birnin Hugue da cewa itace tayi sanadiyyar rasuwar tsohon shugaban, kafin ta yanke masa hukunci.

Daya daga cikin jaridun mai suna Lurid, ta rawaito wani likita na fadin cewa tsohon shugaban ya dade yana fama da matsananciyar rashin lafiya, amma mahukuntan kotun ta kasa da kasa sun ki yarce masa neman magani, bisa dalilin dasu suka barwa kansu sani.

Mr Javier Solana kantoman kungiyyar Eu cewa yayi fatan sa shine wannan rasuwa ta Mr Slobodon ta kasancewa Serbiya darasi na daukar matakan inganta makomarta.

Shi kuwa ministan harkokin wajen sarbiya montengro, Vuk Draskovic, mamaki ya bayyana na yadda mutane ke bayyana ra´ayin su na alhini da tausayi a game da rasuwar tsohon shugaba Slobodon Milosevic, bisa irin rawar daya taka na gudanar da miyagun laifuffuka a lokacin zamanin mulkin sa.

Shi kuwa mai gabatar da kara na kotun kasa da kasar dake birnin Hugue, wato Carla Del Ponte, cewa yayi mutuwar Milosevic, makonni kadan kafin yanke masa hukunci,hakan ba zai hana ci gaban shari´a akan abubuwan daya tafka ba a lokacin mulkin nasa.

A kuwa yayin da magoya bayan tsohon shugaban suke tunanin karrama shi ta hanyar gudanar da jana´izar sa a hukumance a kasar ta serbiya, tuni ofishin shugaban kasar ya fitar da wata sanarwa dake nuni da cewa ba wai ba inke wannan tunani nasu ba mai yiwuwa bane.

Daukar wannan mataki daga ofishin shugaba Boris Tdic dai a cewar bayanai nada alaka ne da zargin tsohon shugaban da suke ne na taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da miyagun laifuffuka a lokacin zamanin mulkin sa.

A yayin da kuwa ake cikin wannan hali, lauyan Milosevic, tabbatarwa da yan jaridu yayi cewa za´a gudanar da jana´izar tsohon shugaban ne a birnin na Belgrade, to sai dai watakila ba a hukumance ba, kamar yadda magoya bayan sa ke muradi.

Mr Slobodon ya dai rasu ne a dakin da ake tsare dashi a ranar asabar din data gabata a sakamakon bugawar zuciya a cewar kotun kasa da kasa dake birnin na Hugue.

To sai dai kuma bincike na dalilin faruwar hakan a cewar kotun na nan naci gaba da gudana.