1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra´ayoyi sun bambamta game da sabbin tsare tsaren Bush a Iraƙi

January 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuUs

Manyan kawayen Amirka a yakin da take yi a Iraqi, wato Birtaniya da Australiya sun yi maraba da jawabin da shugaba GWB ya yi na kara yawan dakarun Amirka a Iraqi. To sai dai dukkan kasashen biyu sun ce ba zasu kara yawan sojojin su a Iraqi ba. FM Australiya John Howard ya yaba da sabbin manufofin Amirka a Iraqi. Howard ya ce shugaba Bush ya zabi hanya mafi dacewa wajen kawo karshen rikicin Iraqi. Ita kuwa sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Margaret Becket ta bayyana ra´ayin gwamnatin ta tana mai cewa ba ko da yake sun goyi da bayan matakan amma ba zasu tura karin soji ba.

Shi ma FM Iraqi Nuri al-Maliki ya goyi da bayan sabbin matakan na Bush. Wani kakakin gwamnati a Bagadaza ya ce muhimmin abu dai shi ne ´yan Iraqi su karbi jan ragamar ayyukan soji a cikin kasar su. Ya ce sabbin manufofin na Amirka ba zasu yi nasara ba idan ba´a shigar da sojojin Iraqi a cikin aikin wanzar da zaman lafiya. A nan Jamus kuwa mai kula da huldodi tsakanin gwamnatin Jamus da Amirka Karsten Voigt ta nuna shakku akan sabbin matakan. Ta ce Jamus ta yi tayin yin amfani da dangantakar da Syria da Iran domin a su shiga cikin tattaunawar warware rikicin Iraqi ta hanyoyin diplomasiya.