1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra´ayoyi sun fara fitowa a game da jawabin Mr Bush

Ibrahim SaniSeptember 7, 2006

Kasashe daban daban na bayyana ra´ayoyin su a game da jawabin shugaba Bush na Amurka

https://p.dw.com/p/BtyK
Mr Bush na Amurka
Mr Bush na AmurkaHoto: AP

A misali kasar Sin fitowa tayi karara ta suki lamirin kasar ta Amurka,game da yadda tace tana tafiyar da gidajen kurkuku na sirri da sunan yaki da ayyukan ta´addanci.

A cewar kakakin ma´aikatar harkokin wajen kasar ta Sin, Mr Qin Gang, kasar ta sin ta kuma suki lamirin yadda ake gallazawa fursunoni da ake tsare dasu a ire iren wadan nan gidajen kurkuku.

A cewar mahukuntan na Sin, abu ne daya zama wajibi ga mahukuntan na Amurka na su daraja kudurin Mdd da kuma dokokin kasa da kasa,a yadda take tafiyar da al´amurranta na kasashen ketare.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa kasar ta Amurka ta fuskanci suka sakamakon tseguntawa da wasu jaridu suka yi cewa tana da wasu gidajen kurkuku na sirri inda take tsare da mutanen da ake zargi yan ta´adda ne a kasashen da suka yi kaurin suna wajen azabtar da jama´a.

Kafafen yada labaru dai sun rawaito shugaban na Amurka na jaddada muhimmancin tafiyar da irin wadan nan gidajen kurkuku na sirri, da cewa sun taimaka wajen yadda kasar ke yaki da ayyukan ta´addanci da kuma yan ta´adda.

Idan dai an iya tunawa,a karon farko shugaba Bush na Amurka ya amsa cewa akwai wasu gidajen kurkuku na asiri da kungiyyar leken asiri ta CIA ke gudanarwa a sassa daban daban na duniya.

A game da hakan ne na tambayi daya daga cikin masu fafutikar kare hakkin bil adama a Nigeria, wato Malam Shehu sani yadda yake kallon wannan al´amari, inda yace kamata yayi kasashen duniya su mika kasar ta Amurka gaban Mdd domin hukuntata, kana a daya hannun a saki dukkannin fursunonin da ake tsare dasu a Guantanamo Bay dake Cuba.

Game kuwa da wannan abu daya fito fili, yan majalisar dokokin kungiyyar tarayyar turai, bukata suka mika ga yayan kungiyyar su nasu bayyana inda ire iren wadan nan gidajen kurkuku na sirri suke a cikin kasashen nasu idan da akwai.

A dai shekarar data gabata ne jaridar washinton Post ta rawaito cewa Amurka nada wasu gidajen kurkuku na sirri da take tafiyarwa a kasashen turai.

Rahotanni dai daga Amurka sun rawaito wasu yan jam´iyyar adawa ta Democrat na bayyana ra´ayin su a game da jawabin na Mr Bush.

A misali Senator Charles Schumer na mai ra´ayin cewa shekaru biyar da suka gabata shugaba Bush yayi alkawarin tsaurara matakan tsaro don kare yan kasa, to amma abin sai ya zama akasin haka musanmamma bisa fitowar rahoton harin nan na sha daya ga watan satumba.

Haka shima Senator Robert Menendez daga jihar New Jersey, ra´ayin sa ya bayyana da cewa dogon turanci da Mr Bush keyi a game da halin da ake ciki a iraqi babu abin da zai canja matukar ba a canza taku ba.

Ra´ayi dai hausawa suka ce riga ne, shi kuwa ministan harkokin wajen kasar Australia, Alexander Downer cewa yayi babu shakka ire iren wadan nan gidajen kurkuku na sirri da Amurka take tafiyarwa sun taimaka kwarai matuka a yakin da take da ta´addanci.

A misali minista Downer ya kara da cewa kasar sa ta amfana kwarai matuka,a game da wannan shiri, domin tsare wani mutum a irin gidajen kurkukun sirrin ya taimaka wajen cafke Khalid Sheik Mohd, mutumin da ake zargi na tafiyar da ayyukan ta´addanci a kudu maso gabashin nahiyar Asia,tare da taimakon kungiyyar Alqeda.-