1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra´ayoyin ketare a game da zabe a Jamus

Yahouza SadissouSeptember 16, 2005

Jama´a daga kasashen ketare na bayana ra´ayoyi a game da zabe a kasar Jamus.

https://p.dw.com/p/BvZb

Ranar lahadi ce mai zuwa idan Allah ya kai mu, a ke zaben gama gari, na yan majalisun dokoki a nan kasar Jamus, wanda a sakamakon sa, za´a girka sabuwar gwamnati.

Kamar yada kila kuka riga kuka sani, yan takara 2 ne, su ka shiga gwagwarmaysar maye wannan kujera, wato shugaban gwamnati mai ci yanzu, Geher Schröder, da kuma Angeler Merkel, yar takara jam´iyar adawa ta CDU.

Wannan zabe ya dauki hankullan alúmmar kasa, da ma kasashen dunia, kasancewar a yanzu haka, kiddidigar neman ra´ayin jama´a na nuna cewa yan takara 2 su na kunnan doki na yawan kuri´u.

A kasashen ketare shuwagaabni bas u hito bas u ka bayyana karara wanda su ka fi bukatar ya lashe wanan zabe, dalili da dokoki na diplomatia.

Saidai duk da haka manema labarai sun bukaci jin ta bakain sakataarn harakokin tsaro na Amurika Donald Rumsfeld wabnda mur ya kiya bayana raayin sa, sai dai kawai ya bayana cewa Allh ya shi baiwa mai rabo sa´a.

Idan dai ba a manta huldodi tsakanin Jamus da Amurika sun fuskanci rauni a sakamakon kudurin da Gwamnatin Geher Schrödrer ta yanke na ki aika sojoji a kasar Iraki..

A nata bangare sakatariyar kungiyar gamayya turai mai kulla da takara, ta bayana a fili yiwuwar Angella Merkel ta lasje wanan zabe.

Ta ce idan har hakan ta tabbata to abun zai zama babab tarihi ga kasar Jamus wanda shiner karro na farko da mace z ata rike wanan matsayi mai daraja., mussamn kasancewar ta yaer gabacin Jamus.

Sakatariyar ta bayaan cewa idan Angeller Merkel ta samu sa´aar lashe zaben babban ci gaban ne ga Turai bam a ga Jamus kadai.

Wannan kalamomi na Madame Kroes sun sha samun suka daga jamai´an diploamtia da ita kanta kungiyar Gamaya turai.

Don kare kanta daag waann soke soke, kakakin sakataran takara ta klungiyar EU ya bayaan cewa, ta yi kalamomin ne da matsayin ta, na yar gwagwarmayar ci gaban yaya mata ba na sakataraiyar Eu ba.

A yayin da su ke gabatar da jawaban yakin neman zabe, yan takara 2 sun nuna, burin su, a game da karfafa cudaya da ketare da zaran sun samu nasara a zaben.

Angeller Merkel ta bayana kullar sabuwar hulda da kasar Israela kasancewar ta kasa mai taka raawr a dandali diplaomatia na dunia da kuma harakokin cinikaya.

Angelle Markel ta bayana adawar ta shigar Turkiyy aa kungiyar Ganaya Turai to saidai ta na mai burin ganin an karffafa danganta tsakanin Turkiya da Jamus.

A yayin da Geher Schröder ke daya daga shuwagabanin EU da su ka nuna goyan baya ga shigar Turkiyya a rukunin wanan kaasshe.

A nasu gefe, al´ummmoin kasar Fransa na nuna dari dari, ga yar takara Angeller Merkel, domin masharahanta na nuni da cewa idan ta ci zaben, killa huldodin kut da kut tsakanin Fransa da Jamus sun dan raunana, duk da cewa ta yi alkawarin ci gaba da alakar cude ni in cude ka da Fransa.

A daya hanun kuma maus sharhi na hasasnshen cewa idan Angeller Merkel ta ci zaben za a samu wani saban babe na huldodi tsakanin Jamus da Amurkia.

A yanzu dai hankullan jama´a su karkata mattuka gayya wajen wananzabe da za yi jibi idan ya kai mu.