1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: An rage farashin kayan masarufi

Abdoulaye Mamane Amadou/ SBMay 20, 2016

Gwamnatin Jamhuriyar ta Nijar ta gana da 'yan kasuwa kan batun matakan karya farashin kayayyakin abinci da na more rayuwa gabanin watan azumin watan Ramadan.

https://p.dw.com/p/1Is3E
Niger Marktszene
Hoto: DW/M. Kanta

Taron na yini daya dai da ya tattara 'yan kasuwa musamman ma masu shigo da kayayyakin masarufi, a karkashin jagorancin majalisar 'yan kasuwar kasar da kuma sa'idon kungiyoyin kare hakin masu saya da masu sayarwa. Babbar manufar dai ita ce ta tallafa wa da kuma jan hankalin 'yan kasuwar da su karya farashin kayayyakin masarufi da suke shigo wa da su gabanin da ma lokacin watan azumin Ramadan. Bayan wata doguwar mahawara ce dai tsakanin su, 'yan kasuwar suka daukar wa gwamnati alkawarin tsaida farashi na bai daya don ganin masu karamin karfi sun wadata a wannan wata. To ko yaya gwamnatin taji da alkawuran da 'yan kasuwar suka dauka? Alhaji Alma Oumarou Ministan bunkasa harkokin kasuwanci a Jamhuriyar Nijar ya yi tsokaci kan haka:

Niger Land und Leute Markt in Niamey
Hoto: AP

"Allah ya sa yanda suka dauki wannan alkawarin, su cika shi kuma gwamnati tare da 'yan gwagwarmaya muna masu godiya, sannan mun ce su saka idanu don kar a samu tashin farashi."

Sai dai da yawa daga cikin magidanta sun yi tsokaci kan wannan lamarin inda suka nuna rashin gamsuwarsu da wannan ganawa, inda suka ce an jima ana irin wannan taro amma daga bisani sai a wayi gari da tashin farashin kayayyakin masarufi. Wannan ganawa dai na zuwa ne a yayin da hukumomin kasar suka soke cibiyar binciken kayayyakin abincin da ake shigo wa dasu kasar daga kasashen waje abubuwan da suka jefa dimbin jamaa a cikin fargaba duba da alkawuran da 'yan kasuwar suka daukar wa gwamnati na rakiyar jamaa a watan na Ramadan da farashi mai rahusa