1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rage kudadan bulaguro na ma'aikata a Najeriya

Salissou BoukariApril 7, 2016

Ofishin ministan kudi na Tarayyar Najeriya ya sanar da aniyar gwamnatin kasar ta neman rage kashe-kashen kudi a fannin bulaguron manyan ma'aikatan gwamnati.

https://p.dw.com/p/1IR9Y
Muhammadu Buhari steigt aus einem Flugzeug
Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: GettyImages/AFP/M. Safodien

Ofishin ministan kudi na Tarayyar Najeriya dai ya sanar a ranar Laraba cewa, ya kyautu nan gaba manyan ma'aikatan gwamnatin kasar su sake duba dabi'ar nan ta bulaguro a sashe mai tsada na jiragen sama na first class, domin su dawo ga sashe mai matsakaicin kudi na business class wanda yin hakan a cewarsa, zai sa gwamnati ta samu ragowar wasu kudade da yawansu zai kai Naira miliyan dubu 13 da miliyan 88 kan kudadan bulaguron da gwamnati take kashewa kan manyan ma'aikatan nata.

Wannan mataki dai zai shafi ministoci, da manyan sakatarorinsu, da kuma sauran manyan ma'aikata a wasu fannoni na ma'aikatun kasar ta Najeriya a cewar kakakin ofishin ministan kudin kasar Fetus Akanbi, inda ya ce wadannan kudade da za a yi tsimin su ta wannan hanya, za su taimaka wajan aiwatar da ayyukan bunkasa rayuwar al'umma da kasar ta sa wa gaba.