1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rage yawan sojojin Amirka a nahiyar Turai

Mohammad Nasiru AwalAugust 17, 2004
https://p.dw.com/p/BvhG

Dole kasashen nahiyar Turai su koyi yadda zasu dauki nauyin aiwatar da manufofinsu na tsaro da kansu. Wannan dai wani darasi ne mai muhimmanci da za´a koya daga matakin rage yawan dakarun Amirka a nahiyar Turai. Hakan kuwa ya hada da kara ba juna hadin kai a manufofin tsaro, dubarun yaki da kuma kera makamai tsakanin kasashen Turai.

Janye sojojin Amirka dai ba zo a ba zata ba. Domin wannan daula guda daya da ta rage a duniya na bukatar sahihan canje-canje a manufofinta na tsaro ta yadda zasu dace da kalubalen wannan zamani. Amma kamar kullum kasashen Turai na sako-sako da daukar managartan matakai don tinkarar sabon yanayi na fargaba da aka shiga ciki. Ba su da karfin zuciyar ba juna cikakken hadin kai wajen ingantan tsaronsu da kuma na sauran yankunan dake makwabtaka da su. Kusan ko-wace kasa kan yi gaban kanta a manufofin da suka shafi tsaro, amma ya zama wajibi su koyi darasin yin wani abin a zo a gani daga wannan mataki na janye dakarun Amirka daga Turai.

Ko shakka babu shirin kirkiro wata rundunar kundunbala ta Turai mataki ne akan turbar da ta dace. Yanzu haka dai sojojin Turai na ba da gudummawa a yankin Balkan da kuma a wasu yankuna na wajen Turai da ake fama da rikici kamar kasar Afghanistan. Ko da yake matsalolin karancin kudi na kawo cikas ga ayyukan samar da wata manufar tsaro ta bai daya, kamar a shirin nan na kera jiragen yakin Eurofighter, amma duk da haka kamata yayi su himmatu wajen ba juna hadin kai a fannin aikin soji.

To sai dai kuma bai kamata a yi riga malaman masallaci ba, domin har kwana gobe kasashen Turai membobin kungiyar tsaro ta NATO zasu ci-gaba da dogara kan fasahohin Amirka. Haka zalika Amirka zata bar wasu dakarunta a tsohuwar nahiyar Turai. Kana kuma zata kafa sabbin sansanonin soji a kasashen gabashin Turai kamar Bulgaria da Poland.

Janye sojojin Amirka kimanin dubu 30 daga Jamus bai da nasaba da adawar da Jamus ta nuna da yakin kasar Iraqi. Domin tun a watanni da dama da suka gabata gwamnatin Amirka ta sanar da gwamnati a birnin Berlin wannan shiri na janye sojojinta daga Jamus, wanda za´a fara a cikin shekara ta 2006. Tun a cikin shekarun 1990 Amirka ta fara janye dakarunta daga Jamus. Daga cikin sojoji dubu 250 a da yanzu sauran dubu 73. Jihohin Bavaria da Baden-Württemberg da Hesse zasu fi jin radadin janye dakarun Amirka. Domin suna ba da gagarumar gudummawa a fannin tattalin arziki da samar da aikin yi ga dubun dubatan mutane a wadannan jihohi.

Ba dai nahiyar Turai ce kadai wannan abun ya shafa ba, a nahiyar Asiya ma Amirka zata janye dakarunta don ta sake ba su horo a yakin da take yi da ta´addanci. Wannan mataki kuwa zai taimakawa shugaba GWB a zaben shugaban kasar Amirka da za´a yi a karshen wannan shekara.