1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahotan Amnesty kan rikicin Lebanon

Zainab A MohammedAugust 23, 2006
https://p.dw.com/p/Btyb
Amnesty International
Amnesty International

Kungiyar kare hakkin jamaa ta Amnesty International ta zargi Izraela da keta dokar kasa da kasa da aiwatarda laifuffukan yaki ,saboda lalata yankunan fararen hula da tayi lokacin yakinta da yan Hizbollah a kasar Lebanon.

Kungiyar kare hakkin jamaan tace akwai bayanai da shaidu isassu a dangane da irin hare haren da Izraela takai,da kuma adadin fararen hula da suka jikkata,wanda Izraelan tace tana sane dasu domin hakan yaki ya gada.

Kungiyar Amnesty wadda wakilanta suka lura da yadda wannan fada ya gudana tsakanin dakarun Izraela da yan Hizbollah ,tace Izraela ta keta dokar kasa da kasa na kai hari kai tsaye wa yankunan fararen hula,wanda sakamakon haka suka lalata wuraren more rayuwan alumma babu gaira babu dalili.

Adangane da hakane Donatella Rovera,wadda ta gudanar da bincike kuma daya daga cikin wadanda suka rubuta wannan rahotan,ta bukaci mdd data gudanar da bincike a dangane da irin rawa da Izraelan da Yan Hizbollah suka taka,ayayin fafatawar tasu na tsawon wata guda.

Rahotan da kungiyar wadda keda ofishin a London ta gabatar dangane da rikicin na Lebanon,na nuni dacewa bangarorin biyu sun sabawa dokar kasa da kasa ta hanyar take hakkin biladama ,koda yake da gangan izraela ta kai hare hare kann wuraren more rayuwa na farar hula,da sunan kaiwa yan shiawa hari.

Mataimakiyar babban sakataren kungiyar Kate Gilmore tace babu kanshin gaskiya adangane da bayanan da Izraela tayi nacewa hare haren data kai na bisa kaida.

Tace binciken da suka gudanar,sun gano cewa an tabka laifuffukan yaki da dama a kasar Lebanon.

Amnesty tace ayayin wannan bincike nata,ta tuntubi hukumar tsaron Izraela da gwamnatin Lebanon da jamian mdd.

Kungiyar tace bayan tattara wadannan bayanai da rahotannin ne,ta gabatar da wannan rahoto nata.

Adangane da hakane Kate Gilmore tace dole ne a gudanar da bincike a bangarorin biyu ,domin dukkan fararen hula dake kasashen biyu na bukatar adalci.kuma cikin gaggawa,saboda irin taadi da akayi.

Rikicin dakarun Izraelan da yan Hizbollah na kwanaki 34,wanda ya samo tushe daga sace sojin Izraela biyu da yan Hizbolla sukayi a harin kann iyakokin kasashen biyu a ranar 12 ga watan yulin daya gabata,yayi sanadiyyar mutuwan yan Lebanon 1,300,akasarinsu kuwa fararen hula,da kuma yahudawan Izraela 160,wadanda su kuma akasarinsu sojoji ne.

Bugu da kari sama da mutane dubu 900 suka rasa matsugunnensu daga irin munanan hare haren boma bomai,wanda kwararru ta fannin tattalin arziki suka kiyasta cewa,yayiwa lebanon asarar akalla dala billion 3 na kayayyakin da akayi asara.