1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahotan Amnesty na 2005 akan hukuncin kisa

Zainab A MohammadApril 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bu0W
Irene Khan,sakatare general na Amnesty
Irene Khan,sakatare general na AmnestyHoto: AP

Sama da mutane dubu 20 ne a sassa daban daban na duniya suka mutu ta hanyar yanke musu hukuncin kisa daga laifuffuka da suka aikata a shekarar data gabata.Amma daga cikin kasashen da aka zartar da wadannan hukuncin inji Amnesty,kasar Sin c eke dauke da mafi yawan wadanda aka kashe,saannan sai Iran ,kana Saudi Arabia ,ayayinda Amurkace kasa ta hudu a jerin kasashen da aka aiwatar da hunkunce hukuncen na kisa.

A Rahotannata na shekara shekara akan hukuncin kisa,kungiyar ta kare hakkin jamaa tace a kasar sin mutane 1,770 ne aka yankewa hukuncin kisa kuma aka zartar a shekara ta 2005,koda yake a hukumance ne hakan,domin kwararru ta fanning sharia daga kasar sunce adadin wadanda aka kashe daga hukuncin sun kai dubu 8.

Rahotan ya kara dacewa akwai sunayen mutane sama da dubu 20 da aka yankewa hukuncin kisa a kasashe daban daban na duniya,duk da kira da takeyi adangane da bukatar dakatar da irin wannan hukunci.

Amnesty bugu da kari tace akalla mutane 2,148 ne aka yankewa hukuncin kisa a shekara data gabata a kasashe 22,kashi 94 daga cikin 100 na yawan wadannan mutane kuwa,an zartar da hukuncin ne a kasashen Sin,da Iran da Saudi Arabia da Amurka.Sai dai tace an samu raguwa daga 3,797 na shekarata 2004,amma ya karu daga na shekarata 2003,inda a wannan shekarar mutane 1,146 ne aka yankewa hukuncin kisa.

Sakatare general na kungiyar Amnesty ta bayyana hukuncin kisa da kasancewa hukunci na karshe mai tsanani,wanda ke take hakkokin biladama,saboda ya sabawa kima da daraja ta dan adam,,wanda inji ta akan zartar da wadannan hukunci ne saboda dalilai na siyasa ,amma ba gaskiya da adalci ba.

Ta kara dacewa a yayinda duniya take cigaba da juya wannan hukunci baya,tare da bukatar a kawo karshensa,a bayyane take cewa kasashen Sin da Iran da Saudiyya da Amurka na cigaba da tsananta aiwatar dashi.

Kungiyar kare hakiin jamaar tace a kasar akan zartar da hukuncin kisa ta hanyar bindige mutum ko kuma yi masa allurer da zata rakashi lahira,ayayinda a saudiyya akan fille kan wadanda aka zartar da hukuncin akansu,kana Iran ta hanyar rataya ko kuma jifa,a Amurka kuwa ana amfani da alluran mutuwa kokuma wutan lantarki.

Kungiyar tace kasashe da yawa sunki bayyana adadin wadanda aka yankewa wannan hukunci domin sirrin gwamnati ne kamar yadda kasashen Sin da Vietnam suka nunar.

Sai dai kungiyar tace baya ga Mexico da Liberia,akwai Karin kasashe 86 da a halin yanzu suka haramta aiwatar da hukuncin kisa,kowane irin laifi mutum ya aikata,idan aka kwatatnta da kasashe 16 a 1977.