1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahotan binciken shirin musayar mai domin Abinci a Iraki daga 1996-2003

Zainab A MohammadOctober 28, 2005
https://p.dw.com/p/Bu4W
Hoto: AP

Hukumar ta musamman mai zaman kanta da aka nada domin binciken shirin nan na musayar mai da abinci a karkashin majalisar dunkin duniya a kasar Iraki ta fid rahotan bincikenta.Rahotan dai na nuni dacewa masu gabatar da kara a kasashe 66 zasu iya gurfanar da kamfanoni 2,200,saboda zarginsu da karkatar da kimanin dala Billion1.8,wa gwamnatin Sadam Hussein na wancan lokaci.

Sakamakon binciken wanda ke cikin rahotan shafuna 623,ya bayyana sama da rabin kamfanonin da suka hada baki da gwamnatin sadam ta hanyar bada cin hanci domin Karin kudaden mai wamda ya basu daman samun kwangilan.

Shugaban hukumar binciken mai zaman kanta, kuma tsohon shugaban hukumar baitul malin Amurka Poul volcker,ya zargi sakatariat mdd da komitin sulhu da kamfanonin da ke cikin shirin da gazawa wajen sauke nauyi daya rataya a wuyansu.

Jerin kamfanoni da ake zargin dai sun hadar dana kasashen Vietnam,da Amurka da fitattun kamfanonin turai kamarsu Siemens da Volvo.To sai dai da hukumar binciken ta tuntubi kamfanonin da yan kwangilan,sun karyata wannan zargi,face kamafani guda daya da kuma wasu yan kwangila 26 dake samarda kayayyaki,inji rahotan.

Bugu da kari rahotan ya kuma zargi Bankin nan na BNP-Paribas na kasar Faransa,wadda ke kula dad ala billion 64 da aka kebe domin gudanar da shirin,da almubazzaranci daga kudaden da kuma gazawa wajen tona asiran wadanda suka sabawa kaidoji.Shi ma wannan bankin ya ki amincewa da zargin da ake masa.

Shirin musayar mai domin abinci da aka fara daga 1996 zuwa 2003 a kasar Irakin dai nada nufin rage radadin rayuwar talakawan kasar,sakamakon takunkumin tattalin arziki da mdd ta kakabawa Iraki,bayan dakarun gwamnatin bagadaza sun kai mamaye kasar Kuwaiti a shekarata 1990.A karkashin yarjejeniyar dai an amincewa Iraki ta sayar da manta domin sayen abinci da magunguna da wasu kayayyakin masarufi.

Daya daga cikin komissiononin hukumar bincike kuma Alkali daka Afrika ta kudu Richard goldstone,zaa gabatar da rubutattun shaidu wa mdd ,tare da jamian tsaro.Ya kara dacewa a shirye suke su bayar da dukkan goyon bayansu ,a dangane bukatun masu gurfanar da kara akan wadannan zarge zarge.

Tuni dai wasu kasashe da suka hadar da Amurka da Britania da faransa da Switzalandsuka fara shirin gurfanar da kararraki.Shugaban kamfanin man Texas na Amurka Oscar Wyatt a birnin New York jiya,ya karyata zargin da ake masa na hadin baki domin bayar da cin hanci na miliyoyin dalolin Amurka a lokacin shirin.

To sai dai Mr Peter Eigen na hukumar yaki da rashawa ta taranparency int dake da headquatanta a birnin Berlin,ya bayyana shakkun yiwuwan gurfanar da wadannan kamfanoni gaban hukuma.

Rahotan hukumasr yayi nuni dacewa daga cikin sama da fadi da akayi na kimanin dala Billion 1.8 na shirin,sadam ya samu dala Billion 11,daga man dayayi fasa kwaurin sa wajen shierin,da masaniyar komitin sulhun mdd,wadda keda alhakin kulawa da shirin.

Rasha wadda tayi adawa da takunkumin da aka kakabawa Irakin a wancan lokaci,itace yar lelen cin gajiyar shirin ,inda ta samu dala Bilion 19,daga cinikin man.Gwamnatin kasar dai ta taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa biyan kudaden ta ofishin jakadancin Iraki dake birnin Moscow da wasu kasashe 9,inji Rahotan.

A bangaren manyan mutane da suka karbi cin hanci kokuma moriyar shirin musayar mai domin abincin na Iraki dai akwai Jean-Bernard Merimee,tsohon jakadan kasar faransa a mdd,wanda yanzu ake bincikensa,kuma rahotan ya bayyana cewa jamiin ya amince kasancewarsa cikin shirin.

Amma wadannan suka ci gajiyar shirin a siyasance sun karyata zargin da ake musu,wadanda suka hadar da Dan majalisar dokin Britania George Gallowaya,da shugaban Robertor Formigoni na Italiada Rev Jean.Marie Benjamin,wani limamin katholika dake zama mataimakin sakataren fadar fafaroma na Vatican,da dai wasu fitattun jamaa.