1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahotan cigaban tattalin arziki akan Afrika

April 3, 2007
https://p.dw.com/p/Btvs
Headquatar hukumar raya tattalin arzikin Afrika
Headquatar hukumar raya tattalin arzikin AfrikaHoto: picture-alliance/ dpa

Ana saran cewa zaa samu ingantuwan tattalin arziki a nahiyar Afrika a shekarata 2007,da kimanin kashi 5 da digo 7 daga cikin 100,wanda ya gaza adadin kashi 7 daga cikin 100 da ake bukata na rage talauci Inji Rahotan mdd.

Rahotan wanda hukumar kula da harkokin tattalin arziki na Afrika ta mdd dukin duniya ta fitar,na kira dangane da bukatar mayar da hankali kan inganta tattalin arziki,tare da rage yawan dogaro kan albarkatun mai.

Kazalika akwai bukatar kasashen Afrika da kungiyoyin bayar da tallafi na kasashen duniya su rage tsananci da sukanyi ayayin basu rance,domin taimakawa kasashen wajen sarrafa albarkatu da suka dasu ,zuwa kyawawan kayayyaki da zasu iya kaiwa kasashen ketare.

Rahotan ya kuma jaddada bukatar hukumomin na agaji ,su rika laakari da matsayin kowace kasa,amaimakon tallafi na tsarin bai daya da sukan bawa wadannan kasashe,domin cimma burinsu na farfado da kananan masanaantu.

Gabannin gabatar da wannan rahotan dai wakilin hukumar Eloho Otobo ya shaidawa yan jarida cewa,tattalin arziki na nahiyar Afrika na samun ingantuwa,amma yana bukatar kyakkayawar kulawa ta kowane fanni.

To sai dai ko tayaya wakilan wannan hukuma suka cimma sakamakon wadannan kasashe da suka gabatar da rahoto akansu?Leonce Ndikumana shine kordinata kan rahotan harkokin tattalin an Afrika a birnin Adisa baba kasar habasha...

“Yace kafin mu cimma gabatar da wannan rahoto,sai da mukayi nazarin dangane da dukkan matakai na tattali da kasuwanci da suka hadarda na kananan masanaantu,da kuma ire iren cigaba ko akasin haka da ake samu.Daga nan ne makayi hasashen bukatu da kuma makomar wadannan yankuna nan gaba”

To sai dai inji Mr Otobo da yawan yake yake dake addaban kasashen Afrika da dama ,masu yin tsare tsare wa wannan nahiya na bukatar suyi nazarin halin da kowace kasa take ciki,shin tana cikin yaki ne,ko kuma akwai alamun barkewar yakin ko kuma tana cikin hali matsananci na siyasa,ko kuma ta dorewar democradiyya.

A bangarensa Mr Ndikumana yace taken rahotan hukumar tattalin na wannan shekara adangane da Afrika yanada matukar tasiri wa halin da nahiyar take ciki.

“abunda muke nufi da taken wannan rahoto shine ,bukatar samarda yanayin da zaa iya sarrafa kayayyaki da albarkatu da wadannan kasashe keda su,wadanda kuma zaa iya shigar dasu a akasuwannin cikin gida kazalika zaa iya fitar dasu ketare.sanin kowane kasashen Afrika sukan yi dogaro kachokan akan albarkatu da suka mallaka kamar na mai ko kuma na kayyakin amfanin gona,wadanda kuma cinikin su yakan taallaka ne akan yadda kasuwannin duniya suke”