1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahotan halin talauci da yunwa a Afrika

October 25, 2007

Kokarin taimakawa kasashen masu tasowa na yakar matsalar yunwa

https://p.dw.com/p/BwXE
Yaki da Yunwa a Afrika
Yaki da Yunwa a AfrikaHoto: FAO

Majalisar dunkin duniya na fatan ganin cewar an yaki talauci da matsalolin yunwa,wanda hakan ke cikin manufofin data sanya gaba.A yanzu haka dai kasashje shida daga cikin 42 dakaye yankin kudu da Sahara na Afrika ne ,suke da damar cimma wannan manufa.

A yanzu haka dai akwai kimanibn jutane billion 6 da rabi a doron kasa.Bisa ga kiyasin hukumar bada tallafin abinci na mdd kuma,ana samun karuwan yawan mutane a doron kasa cikin gaggawa,wanda hakan ya sanya ake fuskantar matsalar karancin abinci.

Kididdiga ya nunar dacewa a nahiyarmu ta Afrika kadai,akwai kimanin mutane million 206 dake fama da matsalar yunwa,wanda ke zama babbar barazana ce wa nahiyar baki daya inji wakilin mdd na musamman dangane da yancin samarda abinci,Jean Ziegler.

Ya bayyana cewar yunwa wata babbar matsala ce dake jefa millioyoyin mutane cikin hali mawuyaci na rayuwa....

“Ziegler yace kowane yaro daya rasa ransa sakamakon yunwa,na mai kasancewa kisan gilla ,wanda kuma ke faruwa kusan kowace rana.Wannan kuwa matsala ce da zaa iya dangana da biladama”

Wannan kisangilla sakamakon yunwa,kamar yadda wakilin mdd Zigler ya bayyana ,yafi yawaita ne a kasashen dake yankin kudu da sahara na nahiyar Afrika.

A kasashe masu tasowa dake yankin Latin Amurka da Asia dai an samu nasara a kokarin yaki da yunwa,amma matsalar ta gagara a kasashen nahiyar Afrikaa dake yankin kudu da sahara,kamr yadda Zoegler ya bayyana..

“A Afrika matsalolin sunyi yawa,wandanda duk suke barazana wa nahiyar,kama daga matsalolin karancin ruwan sha ,mai tsabta ,da matsaloli na rigingimun siyasa da madafan iko ,wadanda duk baki daya,hakan ne ke kasancewa sakamakmo”

Sai dai kasashen wannan yanki na Afrika suna da damar kawo sauyi,domin cimma wannan manufa ta yakar matsalar yunwa da talauci,musamman ta bangaren kasuwanci,tunda damar rigingimun siyasa ne ke haifar da koma baya har ta bangaren nasarar masana’antu dake wannan nahiya,inji wakilin na mdd Jean Ziegler......

“Kungiyar kasashen turai ta gabatar da wata sabuwar yarjejeniya kan harkokin fitar da kayayyaki zuwa ketare.A sheakarar data gabata nedai kasashe masu cigaban masana’antu suka biya manomansu kimanin million 349,amatsayin kudaden ayyuka da kuma rangwamen fitar da kayayyakin gonakinsu zuwa kasuwannin ketare.Hakan na nufin idan yau ka shigar da kayyayakin ka zuwa kasuwannin Afrika, ko kai bajamushe ne ko bafaranshe ne ko dan portugal ne ko kuma daga Italia,zaka iya kwatanta farashin kayayyakin kaa wanda koda da rabin nakan ,zaka iya sayan wasu kayyayaki da ga wajen yanAfrika”

To sai dai wa yan kasashen ta Afrika da dama wannan wata dama ce a bangaren kasashe masu cigaban masana’antu na turai din su ci moriyar kayayyakin da aika noma a ko aka sarrafa a Afrikan cikin ruwan sanyi.Fatoumata Sire Diakie,itace jakadar Mali a mdd..

“A watan Disamba mai gabatowa ya kamata a rattabga hannu a wannan yarjejeniya,wanda keda nufin bude dukkan kasuwannin mu,wanda kuma ko kadan bazaa iya kwatanta su dana kasashe masu cigaban masana’antun ba ,domin bamu da wani abu da zaa iya kwatantawa da nasu”.