1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

RAHOTAN HUKUMAR KYAUTA JIN DADIN ALUMAR DUNIYA

February 25, 2004
https://p.dw.com/p/Bvlh

JAMILU SANI: Cikin wani rahoto da hukumar dake lura da yadda halin na cigaba a duniya ke tasiri kann rayuwar alumar duniya,da kungiyar kwadago ta duniya ta kafa,ta baiyana bukatar dake akwai ta samar da kyawawan manufofin da zasu taimaka wajen ciagban aluma,tare da tabatar da ganin an yi adali wajen aiwatar da irin wadanan manufofi. Hukumar dai ta World Commission on the Social Dimission of Globalasion,dake kokarin ganin an samar da manufofi na cigaban rayuwar aluma,ta la'arai da cigaban da ake samu a duniya a wanan lokacin da muke ciki,ta baiyana bukatar dake akwai ta shiga da majalisar dikin duniya cikin dukanin wani lamari da zai kawo cigaba na rayuwar alumar duniya baki daya.

Tun a ranar talatar data gabata ne dai wanan hukuma ta kyautata rayuwar alumar duniya,ta gabatar da rahotanta mai shafuka 168 a birnin London,wanda kuma ya kunshi fanonin da dama na cigaban aluma a fanin cigban da ake samu a kasahen duniya.

Yan kwamitin wanan hukuma dai sun fito ne daga bangaren kasahe masu arzikin masana'antu da kuma matalautan kasahe masu tasowa,kungiyoyin cinki,yan majalisun dokoki na kasahe,shugabanin aluma,maluma da kuma masu baiwa gwamnatocin kasahe shawara,kamar dai yadda shugaban wana kungiya Halonen ya baiyana haka cikin rahotan da suka fitar na wanan shekarar. Irin wakilcin da aka samu na bangarori da dama a fanin rayuwar aluma,zai taka muhimiyar rawa wajen irin muhawarar da za'a tafka ta kasahen duniya game da irin tasirin da cigaban duniya ta samu ya shafi cigaban rayuwar aluma. Rahotan dai na hukumar dake lura da kyautata rayuwar alumar duniya,ya baiyana cewa majalisar dikin duniya da kuma kungiyoyin dake cikin inuwarta,ya kamata a dorawa alhakin samar da manufofi na cigaba a duniya,musanman ma a fanin cigaban kasuwanci,tabatar da tsaro a kasahen duniya da dai sauran su.

Sun dai baiyana cewa majalisar dikin duniya ce ya kamata ta shirya manufofi na samar da cigaba a tsakanin alumar duniya,ta yadda hakan zai dace da tsarin dokoki na kasa da kasa. Manufofin dai na samar da cigaba a duniya,sune ke taka muhimiyar rawa wajen samar da cigaba na mulki irin democradiya a kasahe,da kuma bunkasar tattalin arziki. Rahotan dai na hukumar kyautata jin dadin alumar duniya,yayi kira ga kungiyoyi na kasahen duniya, da suka hadar da majalisar dikin duniya,bankin duniya,da kuma asusun bada lamuni na duniya,da su hada kai wajen ganin an samar da manufofi na cigaba da zasu shafi bunkasar tattalin arzikin kasahe masu tasowa da kuma kyautata rayuwar alumomin dake zaune a irin wadanan kasahe. Haka zalika sun bukaci a dauki matakan kare hakin maikata,inganta harkokin kula da lafiya,ilimi,abinci,tsaro da kuma uwa uba samar da kyakyawan muhali ga aluma. Wanan hukuma dai ta kyautata jin dadin alumar duniya,na mai ra'ayin cewa kamata yayi kasahe masu tasowa su amfana da dukanin manufofi na cigaban duniya,kamar dai yadda kasahen da suka cigaba ke samar da irin wadanan manufofi na cigaba a kasahen su.