1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahotan kungiyar yaki da rashawa na 2006

Zainab A MohammadFebruary 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bu1v

Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta kasa da kasa ,watau transparency International ta fitar da rahotanta na shekara shekara akan kasashe da akafi tabka rashawa.

Rahotan kungiyar t Ina wannan shekara dai ya mayar da hankali ne kachokan kan irin cin hanci da akeyi a sashin kula da lafiya,wanda kan hana mutane da dama sukunin samun magunguna da suke bukata ,inda inji rahotan hakan kuma yana taimaka tsananta muggan cututtuka da tallafa yadasu.

Kungiyar tace harkokin cin hanci da rashawa da suka mamaye sashin kula da lafiya ,batu ne dake bukatar kashe makuddan kudade saboda illolin dake tattare da hakan,inda ta bada misalign aaran rayukan jarirai wadanda zaa iya ceton rayukansu.

Kungiyar Transparency tayi bayanin cewa duk da hankali da aka mayar wajen kashe makuddan kudade a sashin kiwon lafiya,wannan sashi na cigaba da fama da matsaloli saboda karkatar da kudade da kayayyakin aiki cikin wasu harkoki daban.

Bugu da kari samun jerin sunayen maaikatan karya a maaikatun kula da lafiya na daya daga cikin batutuwa da Transparency ta bayyana da kasancewa ruwan dare a kasashe daban daban na duniya.

Kana ga batutuwa na karban kudade daga jamian asibiti kafin su bawa majinyaci magani,.koda kuwa wannan magani kamata yayi a karbe shi kyauta.bya ga haka wasu jamian kiwon lafiyan na karban kudade ta bayan fage kafin su dubi lafiyar majinyaci.

Akan hakane kungiyar ta taranparency tayi nuni dacewa jamaa su rage darajawa sashin kula da lafiya saboda irin rasahwa da cin hanci daya dabaibaye wannan sahshi.

TI tace dole ne adauki matakai da suka dace wajen ceton wannan sashi dake da muhimmanci ga rayuwar biladama,musamman a bisa kokari da akeyi na yaki da yaduwar cututtuka kamar HIV da malaria da tarin fuka da makamantansu,wadanda duk da dubbin kudade da kasashe ke bayarwa domin tallafi sai dada yaduwa cututtukan sukeyi kamar wutan jeji.

Kungiyar ta bada misalign kasa kamar Kenya,inda manyan jamian dake cibiyar kula da kuma yaki da cutar Aids sukayi sama da fadi da kudaden da aka bada gudummowansu domin cibiyar.Akan irin matsalolin da kasashen nahiyar Afrika ke ciki kuwa ,kungiyar tace dole ne gwamnatoci su mike tsaye wajen taka rawa musamman domin kwace rayukar alummarsu daga annobar cin hanci a sashin kula da lafiya.

Chanthal Uwimana jamia ce a sashin kula da Afrika a heedquatar kungiyar ta Transparency dake birnin berlin tayi .

A kowace shekara mukanyi laakari da sashi mafi muhimmanci guda, awannan shekara mun mayar da hankali ne kan sashin kula da lafiya,kamar yadda abara muka yi nazari kan harkokin cin hanci a kwangila kana bara waccan harkokin siyasa,kuma badi zamu duba sashin sahria.

A kuwa dangane da muhimmancin wannan sashi ,kungiyar ta karbi rahotanni daga kasashe daban daban daban wadaqnda bisa kansu ne ta rubuta wannan rahoto data gabatar

Oton

Sashin lafiya yana da matukar muhimmaci ,idan mukayi laakari da cin hanci da rashawa a wannan sashi,zamuga cewa ana asaran rayukan mutane masu yawan gasket wadankuwa zaa iya ceton rayukansu.Dalili kenan daya sa muka mayar da hankalai wajen kasashen da ake tabka cin hanci a wannan bangare domin karewa talakawan kasashen nasu.