1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Amirka kan tarzoma

Bergmann, Christina (DW-Washington)May 1, 2008

Har yanzu ƙungiyar al-Qaida na zama babbar barazana ga Amirka da sauran ƙawayenta

https://p.dw.com/p/DroS
Shugaba BushHoto: AP

A cikin rahotonta na shekara shekara game da ta´addanci da ta bayar jiya, gwamnatin Amirka ta yi tsokaci game da haɗarin ta´addanci daga ɗaiɗaikun ƙasashe da ƙungiyoyi. Ta ce ko da yake yawan hare haren ta´addanci sun ɗan ragu a duniya baki ɗaya, amma yawan mutane da ke mutuwa sakamakon ayyukan tarzoma ya ƙaru. Mohammad Nasiru Auwal na ɗauke da ƙarin bayani.


A Iraqi kaɗai mutane kimanin dubu 44 aka kashe ko aka yiwa rauni ko aka yi garkuwa da su a bara, wato fiye da rabin yawan mutanen da ayyukan ta´addanci suka rutsa da su gaba ki ɗaya. Rahoton ma´aikatar harkokin wajen Amirka ya nunar da cewa Iraqi ta fi ko wace kasa fama da hare haren ´yan ta´adda. Mai kula da aikin yaƙi da ta´addanci a ma´aikatar harkokin wajen Amirka Dell Dailey ya ce idan aka kwatanta da bara waccan, a shekara ta 2007 an samun ƙarin mutane dubu biyu da suka mutu a duniya baki ɗaya duk da raguwar yawan hare-haren ta´addanci. Ya ce hakan na da nasaba da ƙaruwar ´yan harin ƙunar baƙin wake.


1. Dailey:

Ya ce "Abin baƙin ciki ne yadda ´yan tarzoma da ke sadaukar da rayukansu kai ɗaukar ko wane irin mataki na ganin sun halaka mutane da yawa."


To amma duk da haka an samu ingantuwar tsaro a duniya, inji Dailey.


2. Dailey:

Ya ce "A kullum ƙasashen duniya na yiwa dokokin yaƙi da ta´addanci kwaskwarima musamman wajen yaƙi da masu tallafawa ta´addanci da kuɗi. Hukumomi da ´yan sanda na faɗaɗa ayyukansu tare da taimakon ƙasashe maƙwabta ko ƙungiyoyi na ƙasa da ƙasa."


To sai dai har yanzu ana fuskantar barazanar ´yan tarzoma. Yayin da yawan hare haren ta´addanci suka ragu a yankin Gabas Ta Tsakiya da Indiya da Indonesia, amma sun ƙaru a ƙasashen Somalia da Afghanistan, yayin da a Pakistan ya ninka har sau biyu inji rahoton. Har yanzu kuwa ƙasashen Kuba, Koriya Ta Arewa, Sudan, Syria da kuma Iran na a jerin ƙasashen da Amirka ke zargi da tallafawa ´yan tarzoma.


A nahiyar Turai kamar yadda Dailey ya yi bayani, ana samun ƙaruwar aikace aikacen ´yan tarzoma, to amma ƙasashen Turai na da ƙarfin shawo kan wannan matsala.


3. Dailey:

Dailey ya ce "ɗaukacin ƙasashen Turai na da yawan baƙi musulmi. Idan aka kyale su ba a shigar da su cikin harkokin yau da kullum ba to suna iya zama wani dandalin nuna rashin gamsuwa."


Cikin sauƙi hakan ka iya haifar da ƙungiyoyi irin na masu tsattsauran ra´ayi. Da yawa daga cikin ƙasashen Turan sun san da haka shi ya sa suke ƙara ɗaukar sahihan matakan shigar da waɗannan tsiraru a cikin jama´ar ƙasa. Dailey ya ce ko da yake ƙungiyar al-Qaida ba ta ƙarfi kamar gabanin 11 ga watan Satumban shekara ta 2001, amma har yanzu tana zama babbar barazana ga Amirka da sauran ƙawayenta.