1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton assusunn bada lamani na dunia a game da ci gaban kasashen Afrika

Yahouza sadissouOctober 11, 2005

Assusun bada lamani na dunia ya hiddo rahoto a game da ci gaban kasashen Afrika a shekara ta 2006

https://p.dw.com/p/BvYu

Jiya ne a birnin Ikkon Nigeria, assusun bada lamani na dunia ya hiddo rahoto a game da makomar ci gaban kasashen Afrika a shekara mai zuwa ta 2006.

A cikin wannan rahoto,mataimakin daraktan assusun Michel Novack, ya sannar cewa : a shekara mai zuwa sakamakon hauhawar parashen dayan mai a kasuwanin dunia, za a samu ci gaba ta fannin tattalin arziki, a wasu kasashen Afrika na yankin kudanci Sahara, to saidai, wannan ci gaba, ba za shi kai mizanin da Majalisar Dinkin dunia ta kayyade ba,na yaki da talauci.

A jimilce Afrika za ta samu Karin ci gaba na kashi 5 da dugu 3 bisa dari, a yayin da a shekara da mu ke ciki, kiddidiga ta nuna cewa, cigaban bai wuce kashi hudu da dugu 6 ba.

Saidai, a hannu daya, kasancewar gibin da ke dakwai tsakanin karuwar jama´a, da tattalin arziki kasashen na Afrika, ba za su cimma burin kwattata rayuwa ba, na Millenium Development Goals da Majalisar Dinkin dunia ke dauke da shi.

Rahoton yace a kasashen da ke hakko man Petur, ma´aunin ci gaban ya nuna da za su samu karuwa, ta fiye da kashi 8 bisa 100, a maimakon kasa ga kashi 5 bisa 100 a shekara bana.

Kasashen da za su ci moriyar wannan garabassa sune, Angola da Tarayya Nigeria, inji rahoton na assusun bada lamani.

Ya kara da cewa kasashe masu fuskantar yawan karuwar jama´a kamar Taraya Nigeria , ba za su samu wata sa´ida ba ta fannin yaki da talauci, muddun ba su kai mizanin, Karin kashi 10 bisa 100 ba ,na tattallin arzikin su, a ko wace shekara, har tsawon shekaru 10.

A kasashen Nigeria da Angola sabin rijiyoyin man petur da ake ci gaba da ganowa, da kuma karuwar bukatar man a kasuwanin dunia, babu shakka za taimaka, wajen samun haske a harakokin wannan kasashe.

A daya hannun, Afrika ta kudu, da ta yi wa sauran kasashen Afrika fintinkau ta hanyar tattalin arziki, zata tsaya matsayin ta, a dalili da karuwar bukatocin ta,na ci gida.

Wannan ci gaba ya shafi wasu kasashen Afrika, da ba su da arzikin man petur, amma su ka bullo da sabin husa o´i.

Kasashen sun hada da Cap Vert, Madagaskar, Malawi, Mozambique da Saleo.

Su kuwa kasashe masu sayo man petur, daga ketare kamar su Burkina faso, Kenya da Komores, za su samu matsaloli dalili da karuwar parashen man a kasuwannin dunia.

Wasu kasashen kuma, kamar su Lesoto, Seyschelles, Swaziland, da Zimbabwe da kar!! da jibin goshi, za su kai mizanin kashi 2 bisa 100 na ci gaba, a shekara mai zuwa.

A jimilce dai ,inji rahoton na assusun bada lamani, duk da alamomi kyawawa, da a ke gani a nahiyar Afrika, riginginmun siyasa da karancin abinci, da nahiyar ke fuskanta, kan iya mayar da hannun agogo baya, a game da haka abu ne, mai matukar wuya, a cimma burin majalisar dinkin dunia, na kakkabe talauci daga nahiyar Afrika, kamin shekara ta 2015.

Bugu da kari,cutar kanjamaw da ta zama ruwan dare a Afrika ta zama gagarabadaw, ta hanyar nakasa tattalin arziki.

Rahoton ya bayyana barazanar tashe tashen hankulla da ke daidaita wasu yankunan na Afrika, kamar su Jamhuriya Demokradiyar Kongo, da kuma Ruwanda da Burundi, da Uganda, inda duk da yar kwanciyar hankalin da ka samu ake zama cikin faduwar gaba.

A karshe rahoton na IMF, ya yi gargadi ga kungiyar gamayya turai, a game da kuddaden da ta ke bada wa tallafi ,ga manoman rake na nahiyar turai,wanda zai nakasa takwarorin su, na kasashen Afrika.