1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton binciken abin kunya dangane da Majalisa Dinkin Duniya

Mohammad Nasiru AwalSeptember 7, 2005

Shugaban kwamitin binciken Paul Volcker ya yi kira da a samarwa majalisar shugabanni na kwarai

https://p.dw.com/p/BvZr

A hakikanin gaskiya jami´an MDD na kurkusa da babban sakatare Kofi Annan sun so su hana hakan faruwa, wato ba da sakamakon wannan bincike na wani mai zaman kansa jim kadan gabanin taron kolin M ta DD. To sai dai rahoton binciken bai samu babban sakataren da laifi a wannan abin kunya na shirin sayar da mai a saye abinci ba. Rahoton mai shafuka kusan dubu daya bai nuna wata alaka tsakanin Annan da wani ba duhu a harkar dan sa wato Kojo Annan ba.

To amma rahoton yayi suka da kakkausar lafazi akan shugabanci da kuma tsarin gudanarwar a ofishin babban sakataren na MDD. Saboda haka rahoton bai yi wani cikakken bayani game da daidaikun mutane ba, illa kawai yayi magana ne kan ba da wata gudummawa wajen sake fasalta gamaiyar ta kasa da kasa.

Yin haka tun daga sama zuwa kasa shi ne abu mafi a´ala domin ba ofishin babban sakataren ne kawai ya sha wahalar tafiyar da wannan gagarumin aikin taimako na dubban miliyoyi ba, a´a shi ma kwamitin sulhu ya rasa makama. Hakan ne kuwa ya ba Saddam Hussein da kuma wasu ma´aikatan MDD damar yin rubda ciki da kudaden. Shugaban kwamitin binciken kuma tsohon shugaban babban bankin Amirka Paul Volcker da ma´aikatansa sun zargi wasu kasashe masu ikon hawa kujerar naki da laifin amfani da shirin taimakawa Iraqi don azurta kansu da kansu.

Yayin da Amirka ta nuna halin ko in kula wajen sumogar man fetir din Iraqi, ita kuwa Faransa da Rasha sun mayar da hankali ne wajen nemawa kansu kwagila mai riba daga gwamnatin Bagadaza. A wasu lokuta ma wasu sassa da ba su da muhimmanci a cikin majalisar sun yi ta gaban kansu, inda suka yi ta fatali da dokokin MDD. Wani masali maras dadi a nan shine shugaban shirin ba da taimako da kuma wasu ´yan diplomasiyar Rasha su biyu da a yanzu haka suke tsare a birnin New York.

Da yake aikin kwamitin shi ne gudanar da bincike a madadin MDD amma ba ya gurfanad da wani gaban shari´a ba, Paul Volcker yayi kira da a gudanar da managartan canje canje a cikin majalisar kanta. Shugaban kwamitin binciken ya ce ya zama wajibi a sake yin tunani akan aikin babban sakataren MDD musamman wanda ya shafi siyasa. Dole a samar da shugabannin kwarai tare da kirkiro wani tsarin bincike musamman akan ayyukan sannan kuma a faiyace ainihin aikin kwamitin sulhu, don gano abubuwan dake hana ruwa gudu a shirin yiwa MDD kwaskwarima. Volcker ya yi kira da a fara aiwatar da canje-canje a badi, to amma kafin sannan kwamitinsa zai bawa hukumomin shari´a na kasa da kasa jerin sunayen kamfanoni da kuma bankunan kimanin dubu 4 da 500 da suka taka rawa a wannan badakala.

Yanzu haka dai kamfanin Cotecna kadai aka an bata. In dai za´a iya tunawa jim kadan bayan da kamfanin ya dauki dan Kofi Annan wato Kojo Annan aiki, MDD ta ba wannan kamfani dake kasar Switzerland kwangila a Iraqi. Ko da yake ba shaida cewar babban sakataren ya yi amfani da matsayinsa don ba da wannan kwangila, to amma dansa yayi amfani da sunan Annan wajen samun alfarma, ba ma kawai wajen sayen motar marsandi akan farashin da ake ba jami´an diplomasiya ba.