1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton binciken faduwar jiragen sama a Nigeria

April 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1p

Rahoton farko da maáikatar kula da jiragen sama ta Nigeria ta fitar ya ɗora alhakin haɗura biyu na jiragen sama da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 223 a ƙasar a bara, ga rashin kyawun yanayi. Kamfanin dilancin labarai na Nigeria ya ruwaito maáikatar sufurin jiragen sama na ƙasar na danganta haɗuran da suka auku, da guguwa mai ƙarfi da kuma wasu dalilai daga indallahi. Ministan sufurin jiragen sama na Nigeria Babalola Borishade ya ce ana iya samun wasu dalilai waɗanda suka taimaka wajen aukuwar haduran. Zaá gabatar da cikakken rahoton binciken faruwar haɗuran, a cikin watanni biyu masu zuwa. A ranar 22 ga watan Oktoba wani jirgin fasinja ƙirar Boeing mallakar kamfanin Belview ya faɗo jim kaɗan bayan tashin sa daga filin jirgin saman jihar Lagos, inda ya hallaka mutane 117. Kana a ranar 10 ga watan Disamba, wani jirgin ƙirar DC 9 na kamfanin Sosoliso ya faɗo a garin Port Harcourt inda fasinjoji 106 yawancin su yara yan makaranta suka rasa rayukan su. Tun bayan aukuwar haɗuran, shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo ya umarci yiwa ɓangaren sufurin jiragen saman garanbawul domin tabbatar da inganci da kare rayukan jamaá.