1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton haɗin gwiwar ƙungiyoyi masu zaman kan su a game da rikicin tawaye a arewancin Uganda

March 30, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3i

Haɗin gwiwar ƙungiyoyi masu zaman kan su a ƙasar Uganda, sun bayyana wani rahoto a sahiyar yau, a game da tashe tashen hankullan da su ka biyo bayan yaƙin bassasa a arewancin ƙasar.

Rahoton ya ce, ko wane sati, mutane 146 ke rasa rayuka a tashe tashen hankullan da su wakana a arewacin wannan ƙasa.

Rahoton ya ƙara da cewa, a tsawan shekaru 20 na yaƙin bassasa a yankin, ƙananan yara 25.000 a ka yi awan gaba da su.

Kazalika, ako wace rana, a lokacin da yaƙin ya yi ƙamari, yara 45.000 ke ƙaura daga ƙauyukan su, zuwa birane, domin samun mafaka.

A jimilce, yara dubu ɗaya, a ka aifa ta hanyar fyaɗe, ga yan mata, da ƙungiyar LRA ta sata a kasar ta Uganda.

Daga ƙarshe, gungun ƙungiyoyin ,da su ka haɗa da Oxfam, Care International, da ƙungiyar Save the Children, sunyi kira, ga Malajisar Ɗinkin Dunia, da ta dubi yankin arewancin Uganda da idon rahama , ta hanayar ɗaukar mattakan kawo ƙarshen yaƙin bassa, da ke ci gaba da ɗaiɗaita yankin.