1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ZANU- PF na take haƙƙin ´yan jarida aZimbabwe

April 20, 2010

Ƙungiyar kare haƙƙin Ɗan Adam ta ƙasa da ƙasa HRW ta bayyana rahoto game da ´yancin ´yan jarida da walwalar jama´a a Zimbabwe

https://p.dw.com/p/N1Qh
Rahoton HRW game da ´yanci a ZimbabweHoto: AP

Ƙungiyar kare haƙƙoƙin bani adama ta ƙasa da ƙasa wato Human Right Watch ta gabtar da rahoto inda ta zargi gwamnatin haɗin gwiwar ƙasar Zimbabwe da rashin cika alƙawarin da ta ɗauka na kyauttata yancin faɗin albarkacin baki.

A watan Satumba ne, na shekara ta 2008 aka shirya wani babban taro a kasar Zimbabwe wanda aka raɗawa suna Global Political Agreement.

Albarkacin wannan taro da ya sasanta rikicin siyara ƙasar, ɓangarorin daban-daban sun yi alƙawarin  tabbara da yancin ´yan jarida.

To saidai shekaru biyu bayan ɗaukar wannan alƙawari, har yanzu ´yan jaridar ƙasar Zimbabwe na fuskantar gallazawa injin Tom Porteous na Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam.

"Har yanzu ana nan gidan jiya noman goje game da yancin faɗin albarkacin bakin yan jarida.Alkwarain da Zanu PF ta ɗauka ba ta aiwatar da shi ba."

Rahoton mai  ƙunshe da shafi 26, yace har yanzu jam´iyar ZANU -PF ke riƙe da gaskiyar mulki a wannan ƙasa.A game da haka tana take haƙƙoƙin  aikin jarida matuƙa,tare da yin farfagandar siyasa ga shugaba Robert Mugabe.Bugu da ƙari,jam´iyar na juya jami´an tsaro irin yadda ta ke buƙata.

Saɓanin yadda ta alƙawarta sabuwar gwamnatin bata gudanar da cenjin komai ba, ta fannin ´yancin  aikin jarida.

A tsawan shekarun da suka wuce ba ta bada lasisi ko daya ba an kafa gidan talbajan ko Redio mai zaman kansa.

Babu wata murya illa kawai kafofin sadarwa na gwamnati, dake matsayin ´yan amshin shata ga shugaba Robert Mugabe.

A ƙarƙashin sabuwar gwamnatin aƙalla ´yan jarida 15 aka cafke tare da ƙuntata masu.

A halin  da ake ciki tunni har shugaba Robert Mugabe ya fara amfani da kafofin sadarwar gwamnati domin yaƙin neman zaɓen  shekara ta 2011.

Rahoton yace idan dai ba a gudanar da cenji ba na zahiri, ƙasar Zimbabwe na fuskantar barazana,Tom Proteous yayi karin bayyani:

Idan ZANU- PF ta cigaba da take yancin jam´a, ko shakka babu Zimbabwe za ta sake faɗawa cikin wani mummunan rikicin ta yadda sakamakon zaɓe mai zuwa ba zashi tasiri ba.

A shekarar 2008 fiye da mutane 160 suka rasa rayuka bayan da ZANU-PF ta ƙwace nasara da jam´iyar MDC ta Morgan Tsvangirai ta samu a zaɓen shugaban ƙasa.

A ƙarshen wannan rahoto Human Right Watch tayi kira da babbar murya ga shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu dake shiga tsakanin rikicin Zimbabwe yayi iya ƙoƙarinsa, domin jam´iyar ZANU-PF ta mutunta alƙawuran da ta ɗauka.

Mawwallafi: Husseina Jibril Yakubu Edita: Yahouza Sadissou Madobi