1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Hukumar ƙwadago ta ƙasa da ƙasa.

April 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuMd

Hukumar ƙwadago ta ƙasa da ƙasa, ta bayyana rahoto a game da matsanancin halin da yan ƙwadago ke gudanar da ayyuka a ƙasashe daban-daban na dunia.

Rahotonya nunar da cewa a ko wace shekara ma´aikata fiye da milion 2 ke rasa rayuka a sakamakon cuttukan da su ka ɗauka a lokacin aiki, kokuma a cikin haɗari wurin gudanar da ayyuka.

Wannan rahoto da hukumar ƙwadago ta bayyana, ya ƙara da cewa, a ko wace shekara ma´aikata milion ɗari 2 da 70, ke jin raunuka a bakin aiki.

Wannan al´amari na jawo assara mai tarin yawa ga ci gaba tattalin arzikin dunia.

Hukumar ta bada shawarwari ga kampanomni da masa´antu, a game da matakan rage abkuwar wannan haɗarruruka.

Baban mataki acewar ta shine gunadar da bincike na kayan aiki da lafiyar ma´aikata lokaci zuwa lokaci.