1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Human Right Watch akan fadan luu luu a Congo

Zainab A MohammadJune 3, 2005

Kamfanin AngloGold Ashanti na daga cikin masu wannan rikici.....

https://p.dw.com/p/BvbU
Hoto: AP

Kungiyar kare hakkin biladama ta human right watch dake da matsugninta a birnin New York din Amurka ,ta fitar da wani rahoto dake bayyana yadda ake kokuwan mallakan maadinan luu luu a yankin gabashin janhuriyar democradiyyar congo,ba tare da laakari da munanan hali da mazauna yankin ke fadawa sakamakon wannan fafutuka nasu ba.

Rahotan na kungiyar human right watch mai shafina 159,na bayyana yadda mayaka daga bangarorin adawa da junaa Congo,da gwamnatocin kasashe makwabta da kuma kampanonin kasashe da suka hadar da AngloGold Ashanti,ke rufe idanunwansu dangane da matsalolin dake addaban alummomin yankin,ayayinda suke fadan mallake maadinan Luu Luu.

Bugu da kari rahotan ya yi nuni da yadda kungiyoyin mayaka na kauyuka ke fada domin mallakan inda ake tonon luuluu,tare da kuma irin azabtarwa da miyagun ayyuka da akeyi a hanyoyin dake ficewa da wadannan maadinai,inda suke amfani da kudaden da suke samu daga cinikin luuu wajen sayan makamai na yakan juna.

Rahotan kazalika ya bayyana yadda fitaccen kamfanin na sarrafa luuluu watau Anglogold Ashanti ta kulla dangantaka da kungiyar yan tawayen nan na FNL dakewa mutane kisan gilla,tare da taimaka mata mallakan garin Mongbwalu mai albarkatun luu luu,a gunduwar ituri dake yankin arewa maso gabashin Congo.

Marubuciyar wannan rahoto daga kungiyar ta human right Watch Anneke Van Woundenberg tayi bayanin cewa…

“Mun bayyana yadda fada ke cigaba da mamaye garuruwa dake da maadinan luu da kuma hanyoyin da ake fita dasu ,tare da yadda ake fitar da shi ba bias kaida ba daga Congo zuwa Uganda ,kafin wacewa dashi zuwa manyan kamfanonin turai………”

Rahotan dai ya bayyana munanan abubuwa dake faruwa sakamakon irin wadannan rikici da kan barked a suka hadar da yiwa mata fyade,hukuncin kiza ,kashe kashe na kabilanci da kuma ayyukan tilas a wuraren tonon maadinan.

Van Woudenberg ta nuna takaicinta dangane da yadda kamfanoni fitattu kamar AngloGold Ashanti ke tafi da harkokin kasuwancinsu a irin wadannan yankuna dake fama da yaki.

"A lokuta da dama nida kaina nayi Magana da wakilan kamfanin AngloGold Ashanti.Na kuma bayyana musu yadda kungiyar yan tawaye ta FNL da wasu kungiyoyin mayaka ke take hakkin biladama a Congo.Kuma mun basu wannan rahoto na human right watch ……………………”

Masu bincike na kungiyar kare hakkin biladaman dai suna dauke da rubutaccen shaida na ganawar dake gudana tsakanin kamfanin da shugaban kungiyar yan tawaye na FNL Floribert Njabu,wanda yayi alfarin bayyana irin amincewa da tallafi da suka bawa kamfanin.

To sai dai manajan kula da harkokin jamaa na AngloGold Ashanti dake birnin Johanesburg din kasar Afrika ta kudu Allen Fine,yace ba haka lamarin yake ba….

”muna wannan yanki ne karkashin izinin yantacciyar gwamnatin janhuriyar democradiyyar Congo………”

Human Right Watch ta zargi kamfanin AngloGold Ashanti da biyan dala dubu 8 wa kungiyar yan tawaye ta FNL,da Karin wasu dala dubu daya a shekarar data gabata,dangane da wata yarjejeniya data hadar da kai wasu kayyaki da aka saukar a filin saukan kananan jiragen sama dake yankin.Amma wakilin kamfanin yace basa gudanar irin wannan aiki da baya bias kaida.

Mr Fine yace akwai dakarun kiyaye zaman lafiya na gwamnatin Congo dana MDd da aka girke a yankin.