1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton Human Rights Watch akan kasar Ivory Coast

Hauwa Abubakar AjejeDecember 22, 2005

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch,ta fitar da rahoto game da take hakkin bil adama a kasar Ivory Coast,tana mai kiran Majalisar Dinkin Duniya da ta lakabawa shugabanin yan tawaye takunkumi.

https://p.dw.com/p/Bu36
Hoto: AP

Yakin basasa na 2002,a kasar ya barke ne sakamakon wani yunkurin juyin mulki da ya ci tura,wanda ya raba kasar gida biyu,wato bangaren kudu dake karkashin ikon gwamnati da kuma bangaren arewa dake karkashin ikon yan tawaye.

An dai yi yan watanni ne ana wannan yakin basasa amma baa samu nasarar kulla yarjejeniyar zaman lafiya ba tun daga wancan lokaci.

A wancan lokaci kuwa inji kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch,dakarun yan tawaye dana gwamnati sunci gaba da musgunawa abokan adawarsu,a wasu lokutan har da kisan kai,tare kuma kwace wa farar hula.

Shekara daya da ya gabata,komitin sulhu na majalisar dinkin duniya,ya kada kuriar kafa takunkumai da suka hada da dakatar da kadarori da haramta tafiye tafiye akan dukkan wadanda suke hana ruwa gudu ga batun wanzar da zaman lafiya amma kuma bai aiwatar da su ba,duk da cewa ya sabunta su a makon da ya gabata.

Kungiyar ta kare hakkin bil adama,ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya,data kafa takunkumai akan dukkan wadanda ke da alhakin wadanan laifuka da ta zana,tana mai fadin cewa yin sako sako da majalisar takeyi,saboda tsoron lalata shirin zaman lafiya,maimakon haka,hakan ya kara tsananta cin zarafin jamaa ne tare kuma da yin cikas ga ci gaban siyasa na kasar ta ivory coast.

Kungiyar tace,dakatar da daukar mataki ko hukunci akan wadanda suke da laifi saboda neman zaman lafiya mai dorewa,take hakki ne na wadanda aka zalunta,hakazalika zai kara baiwa azzaluman damar ci gaba da zalunci da sukeyi.

Kungiyar taci gaba da cewa,yan tawaye suna kara samun karfi ta yin anfani da karfi ko wata barazana akan jamaa,ganin cewa ba wata doka ta sharia mai karfi a yanzu,haka kuma tace,aiyukan gwamnati na kawadda munanan halaye,tana yinsu ne kawai a wani bangare na babban birnin kasar Abidjan inda magoya bayan kungiyar adawa ko baki suke zaune.

Ta kara da cewa,kungiyoyin dake goyon bayan gwamnati,wadanda mafi yawansu suke yammacin kasar mafi arzikin koko a duniya,suna ci gaba da musgunawa tare da gudanar da aiyukan taadanci kan alummomin yankin.

Wani maaikacin agaji ya fadawa kungiyar ta kare hakkin bil adama cewa,yan tawayen suna tsare mutane bisa laifuka da basu taka kara sun karya ba,kamar kin biyan kudi akan shingaye da suka kakkafa,ko saboda dalilan siyasa,a wasu lokutan sukan yi fashi da dai sauran laifuka iri dabam dabam,yace adalci ya zama abin saye,ka biya kudi ka samu yancin ka.

Da take bincike akan aiyukan kudancin kasar dake hannun gwamnati ,kungiyar tayi hira da wata mata wadda wani jamiin yan sanda yayiwa fyade,yayinda yake barazanar harbe ta,a garin Duekoue dake yammacin kasar,kodayake daga bisani an dakatar da shi daga aiki bayan ta kai kara,amma ba wani hukunci na sharia da aka yane masa.

Kungiyar cikin bukatunta,tayi kira ga kotun kasa da kasa data aika da tawagarta kamar yadda tayi alkawari shekara guda da ya gabata domin gudanar da bincike akan wadanda suke da alhakin aikata wadannan miyagun laifuka.

Wani shirin zaman lafiya na majalisar dinkin duniya dai,ya samu nasarar nada sabon prime minista a wannan wata,wanda zai shirya zaben shugaban kasa a watan oktoba na shekara mai zuwa,amma har ya zuwa yanzu bai sanarda sabuwar majalisar gudanarwa ba.

Ga kuma sabani da ake samu game da raba madafun iko tsakanin shugaba Laurent Gbagbo da sabon firimiya,Charles Konan banny.