1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton James Schlesinger Akan Kurkukun Abu Ghuraib

August 25, 2004

A jiya talata ne tsofon sakataren tsaron Amurka James Schlesinger ya gabatar da sakanamkon bincikensa akan mummunan hali na azabtar da fursinoni a kurkukun Abu Ghuraib dake birnin Bagadaza

https://p.dw.com/p/Bvh2

A cikin rahoton nasa James Schlesinger yayi batu a game da mummunan yamutsin da aka sha fama da shi a kurkukun kare kukanka na Abu Ghuraib, inda aka rika gana wa fursinonin Iraki azaba ba kakkautawa. A cikin watan mayun da ya gabata ne aka nada tsofon sakataren tsaron Amurkan James Schlesinger da wasu kwararru guda uku domin bin bahasin ainifin halin da aka kasance a ciki a kurkukun dake birnin Bagadaza, kuma sakamakon binciken nasu na kalubalantar shuagabannin soja da na siyasar kasar Amurkan baki daya. James Schlesinger ya karya alkadarin janarorin sojan Amurka dake kokarin kakkabe hannuwansu daga ta’asar azabtar da fursinonin domin dora wa kananan kurata alhakin wannan mummunan ci gaba. A tsanake tsofon sakataren tsaron yayi bayani yana mai cewar:

Ba wasu daidakun mutane ne ke da alhakin wannan cin zarafi ba. Abu ne da ya zama ruwan dare a tsakanin sojojin, wadanda suka rika cin zarafin fursinonin ba gaira ba dalili.

Ya ce an gabatar da kararraki da dama a game da haka a can fadar mulki ta Washington da sauran ma’aikatu na gwamnatin Amurka, amma sai aka yi ko oho da lamarin. Bisa ga ra’ayinsa su kansu kwamandojin askarawan na Amurka suna da rabonsu na alhakin wannan danyyen aiki, musamman ma janar Ricardo Sanchez, tsofon babban kwamandan sojojin Amurkan a Iraki. Wani abin kaico shi ne kasancewar ba wani daga cikin jami'n gwamnatin Amurka da ya fito fili ya gargadi masu tsaron fursinonin kuma a sakamakon haka dukkan kafofi da jami’an gwamnatin da lamarin ya shafa suke da alhakin wannan mummunar ta’asa ta cin zarafin fursinonin Iraki. To sai dai kuma duk da wannan bayani da yayi James Schlesinger ya ki ya ba da wata takamaimiyar amsa a game da ko shin kamata yayi Donald Rumsfeld yayi murabus daga mukaminsa na sakataren tsaron Amurka. Da farkon fari dai ba wanda yayi zaton cewar rahoton na Schlesinger zai fede biri har wutsiyarsa, domin bayani filla-filla a game da mummunan hali na muzantawa da cin zarafin fursinoni da aka fuskanta a kurkukun Abu Ghuraib a saboda haka kwararrun masana suka hakikance cewar, wannan fasa-kwai da rahoton yayi zai yi gagarumin ta’asiri musamman dangane da wadanda ake zarginsu da laifin azabtar da fursinonin. A kuma halin yanzu haka ana sauraron daya rahoton azabtarwar, wanda ya shafi rawar da jami’an hukumar leken asiri na CIA suka taka a matakan azabtar da fursinonin. Bayanai sun nuna cewar akwai wasu karin sojoji da ma’aikata farar fula da kuma likitocin sojan Amurkan da za a daukaka kara kansu dangane da ta’asar azabtar da fursinonin na Iraki.