1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton jami´an leƙen asirin Amurika a game da Irak

August 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuDK

Jami´an leƙen asirin Amurika, sun ƙadamar da wani saban rahoto a game da halin da ake ciki a ƙasar Irak.

Wannan rahoto ya biwo bayan jawabin da shugaba Bush yayi a game da Irak wanda ya kwatanta rikicin ƙasar da na Vietnam.

Wannan rahoto ya bayyana raunin gwamnatin Praminista Nuri Al Maliki, da kuma na jami´an tsaro ƙasar, a game da yadda su ka kasa tabbatar da tsaro.

Masu adawa da siyasar Amurika a kasar Irak, sun bayyana gamsuwa da wannan rahoto ,wanda bisa dukan alamu, zai ƙara basu ƙarfin gwiwar matsa ƙaiimi ga shugaban ƙasar Amurika, na janyewar dakarun sa daga Irak.

Wanda su ka gudanar da wannan bincike, sun yi hasashen cewa, nan da wattani 6 zuwa 12, gwamnatin ƙasar Irak za ta ƙara samun rauni, kuma matakan tsaro za su ƙara tabarbarewa.

Saidai a ɗaya wajen rahoton yayi yaba ƙoƙarin dakarun Amurika, wajen samar da zaman lahia, to saidai akwai sauran rina kaba, a game da burin da Amurika ta sa gaba.