1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton kisan ƙare dangi a Kongo

September 30, 2010

Gobe ne Majalisar Dinkin Duniya ke fid da rahoto akan kisan ƙare dangi a Kongo.

https://p.dw.com/p/PRZO
Taswirar Jamhuriyar Dimukuradiyar Kongo

A gobe ne idan Allah ya kai mu Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya zata bayyana sakamakon shekaru gomai na kisan kare dangi da aka aikata a ƙasar Kongo a lokacin yaƙin da ƙasar ta yi fama da shi daga 1993 zuwa shekara na 2003. Sakamakon wanda ke zargin ƙasashe da dama na Afirka da suka haɗa da Yuganda da Ruwanda da Burundi da kuma Angola kan take haƙƙin bil Adama tuni ya sa aka fara kai ruwa rana tsakanin majalisar da ƙasashen da ke yin watsi da zargin. Miliyoyin jama'a ne dai suka rasa rayukansa a sanadin kisan gilla da sojojin ƙasahen suka yi wa waɗanda ba su san hawa ba ballantana sauka, galibi fararen hula.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita: Halima Balaraba Abbas