1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahoton kotun ƙasa da ƙasa a game da yankin Darfur

June 15, 2006
https://p.dw.com/p/Butt

Shugaban kotun ƙasa da ƙasa ta Majalisar Ɗinkin Dunia mai kulla da lefikan yaƙi, ya gabatar da rahoto jiya laraba, gaban komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia.

Luis Moreno Ocampo, ya bayyana binciken da su ka gudanar a kasar Sudann a game da kashe -kashen jama´ar yankin Darfur.

Shugaban wannan kotu, ya tabatar da cewa an shirya kissan kiyasu ga al´ummomin da ba su ji ba su gani ba, a wannan yanki, kuma kotu zata ci gaba da bincike na zahiri, domin tananatce masu leffi a cikin wannan kissa ta kuma yanke masu hukunci da ya dace.

A ɗaya hannun rahoton na kotun Majalisar Ɗinkin Dunia, ya gano cewa, daga cikin mutane kimanin dubu ɗari 3, da su ka rasa rayuka, a yankin Darfur, da dama sun mutu sanadiyar yinwa da rashin kaukayan mahalli, bayan ƙona gidajen su, da dukiyoyin su.

Sannan, al ´ammuran fyaɗe sun zama ruwan dare a yankin.

A makon da ya gabata hukumar kare haƙƙoƙin jama´a, ta Human Rigts Watch, ta yi tsokaci, a game da tafiyar hawainiyar da kotun ƙasa da ƙasa ke yi, a kan shari´ar Darfur, sannan ta zargi kotun da hukumomin Khartum su ka girka, da nuna san rai, da ko in kulla ga shari´ar.